Dalilin da ya sa aka mayar da "lafiyar iyaye mata da 'ya'yansu da lafiyar kananan yara da ci gabasu" a matsayin babban jigon taron shi ne domin a shekarun baya, 'yan Afirka na fuskantar mummunar matsalar rayuwa a duniya. Lafiyar iyaye mata da 'ya'yansu tana da nasaba da ci gaban Afirka sosai. A wani bangare, yanzu a yankunan Afirka ta Tsakiya da ta Yamma, mutane fiye da miliyan 10 suna fama da karancin abinci. A wani bangare na daban kuma, a sanadiyyar rashin matakan kiwon lafiya masu inganci, yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ya kasance yankin da aka fi samun yawan mutuwar mata masu juna 2 da kananan yara a duniya. Kafin wannan, kungiyar AU ta yi kokarin rage abkuwar mutuwar mata masu juna 2 da kananan yara, ta kuma samu sakamako. Duk da haka, manazarta sun nuna cewa, irin wannan kokari bai taka rawar gani sosai ba saboda kasashen Afirka ba su hada kai sosai ba, ba su yi amfani da karfinsu tare yadda ya kamata ba. Ta haka, a yayin taron shugabannin, ana kuma tattauna yadda za a karfafa gwiwar kasashen Afirka, da yin amfani da kudinsu yadda ya kamata, da kyautata kokarin da bangarorin suke yi, da tsara fasali a karkashin shugabancin kungiyar AU a game da lafiyar iyaye mata da 'ya'yansu.
A yayin bikin bude taron, Jean Ping, shugaban kwamitin kungiyar AU ya bayyana cewa, kungiyar za ta kara daukar matakai, a kokarin rage yawan mutuwar iyaye mata da 'ya'yansu a Afirka. Yanzu kungiyar ta kaddamar da shirin "kokarin ceton rayukan mata masu juna 2 a lokacin haihuwa" a kasashe 13 na Afirka, ta kuma yi shirin tafiyar da shirin a wasu kasashe 8 na daban a Afirka. An labarta cewa, shugabannin Afirka za su tattauna yadda Afirka za ta rage yawan mutuwar kananan yara ,da kyautata lafiyar mata masu juna 2, da tabbatar da manufar samun ci gaba da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara a shekarar 2000 wato M.D.G.. Bisa abubuwan da ke cikin manufar, an ce, ya zuwa shekarar 2015, Afirka za ta rage yawan mutuwar kananan yara da shekarunsu ba su kai 5 a duniya ba da kashi 2 cikin kashi 3, yayin da za ta rage yawan mutuwar mata masu juna 2 da kashi 3 cikin kashi 4.
Har wa yau, baton tsaron lafiyar nahiyar Afirka da ake matukar bukatar warware shi ma ya jawo hankali sosai a yayin taron. Bingu wa Mutharika, shugaban kasar Malawi kuma shugaban kungiyar AU na karba-karba ya yi bayani a yayin bikin bude taron cewa, a shekarun baya, Afirka ta samu nasarori sosai wajen tabbatar da zaman lafiya, amma a wasu kasashe da yankuna a nahiyar, matsalar tsaron kasa tana ci gaba da damun mutane. A watan jiya, an tayar da wani bom a yayin gangamin nuna rashin amincewa da sabon shirin tsarin mulkin kasa a wani wurin shan iska da ke birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, inda mutane da yawa suka jikkata ko kuma rasa rayukansu. Sa'an nan kuma, a ran 11 ga wata, a Kampala da ake shirya taron shugabannin AU a wannan karo, an samu tashe-tashen bama-baman kunar bakin wake har sau 2 a jere da nufin rama wa Uganda da ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Somalia.
A yayin bikin bude taron, Jean Ping ya kuma yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu Afirka na fuskantar mummunar matsalar tsaron kasa. A watan Janairu na bana, Jean Ping ya taba sanar da kaddamar da "shekara ta tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa a Afirka", da zummar sa kaimi kan warware matsalar tsaro a Afirka cikin sauri daga dukkan fannoni, amma wannan na kara bukatar kokarin dukkan kasashen Afirka.
Ana zura idon ganin ko za a fitar da wani shirin a game da tabbatar da tsaron Afirka da batun kula da lafiyar iyaye mata da 'ya'yansu a yayin taron shugabannin da ake yi a Kampala.(Tasallah)