As Sy ya bayyana cewa, yanzu Afirka tana fuskantar jan aiki wajen yin rigakafin yaduwar cutar kanjamau a tsakanin iyaye mata da 'ya'yansu da rage yawan mutuwar mata masu juna 2. Asusun UNICEF na sa ido a tsanake kan yaduwar cutar a tsakanin iyaye mata da 'ya'yansu.
A ganin As Sy, hanya mafi dacewa da za a bi wajen yin rigakafi ko kuma samun nasarar hana yaduwar cutar kanjamau a tsakanin iyaye mata da 'ya'yansu ita ce yin nasarar hana mata kamuwa da cutar.
Yin bincike kan mata masu juna 2 ta fuskar kamuwa da kwayoyin cutar, ba wa masu juna 2 magani, hana shayar da jarirai nonon iyayensu da dai sauransu suna taimakawa sosai wajen hana yaduwar cutar a tsakanin iyaye mata da 'ya'yansu, a cewar wannan jami'i.
As Sy, wanda ya taba aiki a hukumar tsara shiri kan cutar kanjamau ta M.D.D. cikin dogon lokaci, ya kuma kara da cewa, abun farin ciki shi ne yanzu wasu kasashen Afirka suna samun ci gaba wajen yaki da cutar kanjamau. A kasar Botswana, mata masu juna 2 da ake yi musu bincike a asibiti kafin haihuwa, wadanda yawansu ya kai kashi 80 cikin dari ana yi musu bincike ne ta fuskar kamuwa da cutar kanjamau, lamarin da ya sanya samun nasarar hana yaduwar cutar a tsakanin iyaye mata da 'ya'yansu.
Nahiyar Afirka, musamman ma yankin da ke kudu da hamadar Sahara ya zama yankin da aka fi samun mutuwar mata masu juna 2 da kananan yara a duniya a sakamakon karancin sharuddan kiwon lafiya masu inganci. Adadin kididdiga ya shaida cewa, a ko wace shekara, kusan rabin masu juna 2 da suke rasa rayukansu a lokacin da suke da ciki ko kuma a lokacin haihuwa sun fito ne daga Afirka, wadanda kuma yawancinsu suka zo daga yankin da ke kudu da hamadar Sahara.
As Sy ya ba da shawarar cewa, Afirka ba za ta iya rage yawan mutuwar mata masu juna 2 ba, sai ta warware wasu matsalolin da ake tinkara cikin dogon lokaci, kamar kasancewar babban gibi a tsakanin masu kudi da matalauta, da gaza gudanar da harkokin kiwon lafiya yadda ya kamata.
Bugu da kari, tilas ne Afirka ta kara kyautata tsarin kiwon lafiya, amma wannan na bukatar dogon lokaci, kuma ya shafi harkokin kudi da hanyoyin samun magani da kuma masu aikin jiyya. Dukkansu na matsayin babban kalubale ne ga Afirka a halin yanzu.
Haka zalika kuma, a ganin As Sy, nauyin da gwamnatoci suka sauke ya fi muhimmanci ta fuskar kyautata lafiyar masu juna 2 da 'ya'yansu a Afirka. As Sy ya ce, a yayin taron shugabanni na musamman da aka yi a birnin Abuja na kasar Najeriya, shugabannin kasashen Afirka sun sha lasar takobin yin amfani da kasafin kudi da yawansa ya kai kashi 15 cikin dari wajen kyautata hukumomin kiwon lafiya, da zummar hana yaduwar kwayoyin cutar kanjamau da ma cutar, amma duk da haka, ya zuwa yanzu da yawa daga cikin wadannan kasashe ba su cika wannan alkawari ba. Har wa yau kuma, wajibi ne gwamnatoci su tabbatar da gudanar da harkokinsu a fili ba tare da boye kome ba, su kau da cin hanci da karbar rashawa, ta yadda za su iya hana yin amfani da kudin kiwon lafiya a sauran fannoni. (Tasallah)