in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ciyar da masana'antun sassaka na birnin Nantong gaba
2010-07-20 10:35:37 cri
Ibrahim: Hukumar kare mallakar fasaha ta birnin Nantong na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin ta kafa ofisoshinta a kasuwannin sayar da kayayyakin saka domin sa kaimi ga masana'antun samar da kayayyakini saka da su kare ikonsu na mallakar fasaha. Ba ma kawai wadannan ofisoshi suna da ikon yin rajistar ikon mallakar fasahar zayyana sabbin ire-iren zane-zanen da ake yi kan kayayyakin saka ba, har ma suna da ikon daidaita matsalolin satar fasahar da ke kasancewa a tsakanin masana'antu daban daban.

Sanusi: Bisa goyon bayan da gwamnatin wurin ta nuna musu, a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, yanzu wadanda suke tafiyar da masana'antun samar da kayayyakin saka na mai da hankali sosai kan ikon mallakar fasaha, sakamakon haka, masana'antunsu sun samu ci gaba cikin sauri, birnin Nantong ma ya zama wuri mafi girma a kasar Sin wajen samar da kayayyakin saka, kuma ana sayar da kayayyakinsu a duk fadin duniya. Mr. Wu Jun, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta yankin Tongzhou da ke karkashin jagorancin birnin Nantong ya bayyana cewa, "Ko shakka babu, kare ikon mallakar fasaha, tamkar ana kare rayuwanmu ce a kasuwa."

Ibrahim: Me ya sa ake mai da hankali sosai kan aikin kare ikon mallakar fasaha a birnin Nantong? A nan akwai wani labari. A shekarar 1996, kamfanin samar da kayayyakin saka na Dongdixing na lardin Taiwan ya soma sayar da kayayyakin saka a wata kasuwar Nantong. An zayyana sabbin zane-zane iri fiye da dari 1 a kan wadannan kayayyakin saka. Sabo da haka, a cikin farkon wata daya kadai da kamfanin Dongdixing ya kafa kantinsa a wata kasuwar sayar da kayayyakin saka na Nantong, yawan ribar da kamfanin ya samu ya kai kusan kudin Sin yuan miliyan dari. Kuma kayayyakinsa ya burge mutane sosai a kasuwa. Amma ba zato ba tsammani, manoman wuri wadanda ba su da tunanin kare ikon mallakar fasaha sun soma satar wannan ikon mallakar fasaha na kamfanin Dongdixing cikin sauri. Sakamakon haka, kamfanin ya yi hasara sosai a kasuwa. Mr. Ge Chi wanda ke kula da aikin sayar da kayayyaki a kamfanin Dongdixing da ke birnin Nantong ya ce, "Bayan bullowar kayayyakinmu da ke da kyawawan zane-zane a kasuwa, mutane da yawa sun saci fasaharmu. A da, muna sayar da kayayyakinmu da tsawonsa ya kai mita dubu 10 a yini daya kawai, amma bayan an saci fasaharmu, ba mu iya sayar da su a cikin tsawon mako daya ba."

Sanusi: Ganin cewa, babu wata hanyar da ta rege, sai kamfanin Dongdixing ya gabatar da su a gaban hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta birnin Nantong da ba a dade da kafa ta ba a shekarar 1996. Wannan hukuma ta kuma mai da hankali sosai kan wannan matsala. Bisa goyon bayan da hukumar ikon mallakar fasaha ta lardin Jiangsu da ta kasar Sin suka nuna mata, hukumar ikon mallakar fasaha ta Nantong ta je kasuwa domin daidaita wannan matsala bisa doka. Sannan wannan hukumar Nantong ta soma yada ilmin kare ikon mallakar fasaha ga 'yan kasuwa ba tare da kasala ba a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata.

Ibrahim: Ba ma kawai irin wannan aikin yana kare ikon mallakar fasaha ba, har ma ya sa kaimi ga masana'antu da su zuba jari domin kirkiro sabbin kayayyaki, har ma wata sabuwar sana'a ta bullo. Yanzu mutanen da yawansu ya kai fiye da dubu 2 wadanda suka gama karatu a jami'o'in da suka kware a fannin zane-zane sun je birnin Nantong, inda suka kafa ofisoshinsu na yin zane-zane. A 'yan shekarun da suka gabata, wata yarinya mai suna Liu Tsui da ke arewa maso gabashin kasar Sin ta isa birnin Nantong har ma ta kafa ofishinta a birnin bayan da ta yi nazarin sauran kasuwannin sayar da kayayyakin saka a duk fadin kasar Sin. Liu Tsui ta ce, "Idan ba a iya kare ikonmu na mallakar fasaha ba, ba za mu iya kasancewa ba, balle neman ci gaba. A ganina, aikin kare ikon mallakar fasaha da ake yi a wannan wuri ya fi kyau."

Sanusi: A watan Yuni na shekarar 2008, kungiyar kare mallakar fasaha ta kasa da kasa, wato kungiyar WIPO ta yi taron karawa juna sani wajen kare ikon mallakar fasaha a birnin Nantong, inda madam Wang Binying, mataimakiyar babban direktan hukumar WIPO da Mr. Dimiter Gantchev, direktan hukumar kare sabbin dabarun raya masana'antu ta kungiyar WIPO suka yaba wa birnin Nantong wajen kare ikon mallakar fasaha. Haka kuma kungiyar WIPO ta tabbatar da kasuwannin sayar da kayayyakin saka guda biyu da ke birnin Nantong da su zama abin koyi wajen kare ikon mallakar fasaha. Game da nasarar da birnin Nantong ya samu wajen kare ikon mallakar fasaha. Mr. Wang Ziqiang, wani babban jami'in hukumar ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ya ce, "A shekarar 1987, lokacin da manoma 21 suka kafa kasuwar sayar da kayayyakin saka a karo na farko tare da kudin Sin yuan dubu 10 kawai, wannan kasuwa ne da ake sayar da atamfa. Amma bayan aka yi aikin kare ikon mallakar fasaha a kasuwa, wannan ya sa ta zama wata kasuwar da ake kirkiro sabbin fasahohi da samar da kuma cinikin kayayyakin saka, masana'antun samar da kayayyakin saka ma sun samu fasahohin zamani wajen samar da kyawawan kayayyakinsu. A nan, ana iya cewa, aikin kare ikon mallakar fasaha yana da muhimmanci sosai." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China