in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ranar Malawi a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-07-14 14:46:29 cri

A ran 14 ga wata, an yi bikin ranar Malawi a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Ministar yawon shakatawa da naman daji da al'adu ta kasar Anna Kachikho da mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin bikin EXPO na Shanghai Jiang Zhangyun sun halarci bikin ranar kasar Malawi.

Anna Kachikho ta nuna godiya ga taimakon da gwamnatin Sin ta bai wa kasar Malawi a fannin shiga bikin EXPO, ta bayyana cewa, bikin EXPO na Shanghai ya samar da wani kyakkyawan dandali ga kasar Malawi don neman bunkasuwa a fannonin zuba jari da ciniki da yawon shakatawa, kana kasar Malawi za ta kara yin musayar ra'ayi tare da 'yan kasuwa na kasar Sin ta hanyar shiga bikin.

Jiang Zhengyun ya ce, a cikin shekaru biyu bayan da kasar Sin ta kafa huldar diplomasiyya tare da kasar Malawi, huldarsu ta samu bunkasuwa mai kyau. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Malawi domin tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma da karfafa hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki da ciniki, ta yadda za a kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China