in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin mawaka za su rera wakokin gargajiya na gida da na waje a wajen bikin EXPO
2010-07-13 21:36:26 cri

Ranar 21 ga wata, a cibiyar nuna al'adu dake farfajiyar bikin baje-kolin kasa da kasa da ake yi a birnin Shanghai, za'a shirya bikin rera wakoki tsakanin kungiyoyin mawaka na kasashe daban-daban. A wannan lokaci, 'yan wasa da yawansu ya kai 2100 da suka fito daga gida da waje za su rera wakoki kusan 30 na manyan nahiyoyi 5.

Ranar 13 ga wata, a yayin wani taron manema labarai da aka yi, mataimakin ministan shirya ayyuka na hukumar kula da bikin EXPO na Shanghai Mista Jin Tao ya bayyana cewa, bikin rera wakoki tsakanin kungiyoyin mawaka zai kasance daya daga cikin muhimman ayyukan nuna fasaha da aka shirya tun bayan da aka kaddamar da bikin EXPO na Shanghai.

Mista Jin Tao ya ce, a yayin bikin, fitattun kungiyoyin mawaka da kungiyoyin masu sha'awar rera wakoki za su hada kai, haka kuma za'a yi mu'amala tare da cudanya tsakanin mawakan dake cikin farfajiyar da na waje da ita. Baya ga masu sha'awar rera wakoki na kasar Sin, kyawawan kungiyoyin mawaka 9 daga kasashen Turai da na Latin Amurka za su halarci bikin rera wakoki a ranar 21 ga wata.

An ce, wadannan kungiyoyin mawaka 9, fitattun kungiyoyi ne wadanda za su halarci gasar rera wakoki tsakanin kungiyoyin mawaka na kasa da kasa a karo na 6, wanda za'a shirya a wannan wata a birnin Shaoxing na lardin Zhejiang. Za'a fara gudanar da wannan gasa tun daga ranar 15 ga wata, inda kungiyoyin mawaka sama da 480 daga kasashe da yankuna fiye da 80 za su halarci gasannin rera wakoki da yawansu ya zarce 500.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China