in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gasar cin kofin duniya ta Afirka ta kudu shi ne Alfaharin Afirka kuma farin ciki na duniya
2010-07-13 16:44:47 cri

Bayan wata guda mai ban sha'awa, yanzu dai an kammala gasar cin kofin duniya a kasar Afirka ta kudu cikin nasara. ba ma kawai an yi wata kyakkyawar gasar cin kofin duniya ba, har ma an sami nasara kan ayyukan shirya wannan gasa. A sa'i daya kuma, an yi gasar cin kofin duniya a nahiyar Afirka a karo na farko, wannan abin alfahari ne ga nahiyar Afirka, kuma ya kasance abin farin ciki ga duk duniya. Yanzu ga wani rahoton da wakilinmu Li Peng ya ruwaito mana.

Kafin wata daya, yayin da ake magana game da gasar cin kofin duniya, mutane suna zura ido kan batun yanayin rashin tsaro, da matsalar na'urorin zirga-zirga na zamani, da matsalar karancin otel-otel a kasar Afirka ta kudu mai masaukin baki watakila wannan ya sa mutane da yawa suna nuna damuwa ko za a iya yin gasar cin kofin duniya yadda ya kamata a kasar Afirka ta kudu. Amma bayan da aka yi gasa ta karshe, ana iya cewa, babu wata matsala da ta faru, kuma an yi nasara sosai. Game da haka ne, Mr. Irvin Khoza shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin duniya na Afirka ta kudu ya ce, "Wannan ita ce gasar cin kofin duniya mafi kyau a tarihi daga fannoni da dama. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, an magance matsaloli da yawa. An yi dukkan wasanni yadda ya kamata, ba a samu wata matsala ko abubuwan tayar da hankali ba, gasar cin kofin duniya a wannan karo ta yi nasara."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China