Bayan bikin rufewa, Alvado, wani mai sha'awar kwallon kafa na kasar Spain, wanda ya zana tutar kasarsu a fuskarsa, gami da yafa tutar kasar a jikinsa, ya gaya mana cewa, zai halarci wata liyafa tare da abokansa don murnar lashe kofin da Spain ta yi. Ya kara da cewa, 'Muna farin ciki kwarai da gaske, saboda wannan ne karo na farko da kasar Spain ta zo na farko a gasar cin kofin duniya. Lallai, wannan abu ne mai ban mamaki. Za mu je wata liyafa don murnar nasarar da muka samu. Amma, ba mu da isasshen lokaci, sai dai za mu shan giya kadan, daga baya kuma za mu je filin jiragen sama kai tsaye, don mu koma kasarmu.'
Luke Degouveia, wani mai sha'awar kwallon kafa daga kasar Spain ya gaya wa wakilinmu cewa, 'Na taba fada kafin gasar cewa, Spain za ta samu nasara, amma kanina bai yarda ba. A ganina, kamata ya yi kasar Spain ta lashe kofin saboda tana da fitattun 'yan wasa.'