in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2010-07-12 16:28:57 cri

A cikin shirinmu na yau, bari mu duba wani labari da muka samu daga jaridar Aminiya ta kasar Nijeriya, wadda aka fita a wannan mako, inda aka mai da hankali sosai kan barazanar yunwa a Afirka ta yamma.

Jaridar Aminiya ta ce, rahotannin da aka samu a kwanan nan sun nuna cewa, akwai barazanar yunwa a wadansu kasashen Afirka ta yamma. Karuwar labarin rashin faduwar damina abu ne da yake kara tabbatar da hakan. Sabo da karancin kaka da kuma tashin gwauron zabin farashin abinci, tuni wasu kasashen Afirka ta yamma suka fara fama da yunwa. A wani rahoto da kungiyar ba da tallafi ta Birtaniya mai suna Oxfam ta fitar, ta ce, tuni ta kafa wani asusu na neman Fam miliyan bakwai, don taimaka wa akalla mutane dubu dari takwas wadanda ke fuskantar barazanar yunwa a kasashe daban daban na Afirka ta yamma.

Rahoton na Oxfam ya yi gargadi game da karin tabarbarewar halin da ake ciki, wanda ya ce, zai iya shafar sama da mutane miliyan 10 a dai kasashen na Afirka ta yamma. Jamhuriya Nijar na daga cikin kasashen, wacce tuni ta fara fuskantar wannan matsala, ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, sama da mutane miliyan bakwai suna fama da bala'in yunwa a kasar. Tuni wadansu daga cikin mutanen suka fara cin ganye tare da shan gurbataccen ruwa, domin neman kubuta daga yunwa, yayin da dabbobi ke ta mutuwa sabon da rashin abinci.

Jaridar Aminiya ta ci gaba da cewa, duk da cewa rahoton na Oxfam bai kawo sunan Nijeriya kai tsaye a jerin kasashen da ke fama da wannan annoba ba, ba za mu dauki kanmu wadanda ke da wata garkuwa ga halin da ke addabar makwabtanmu ba. Ba wai kawai daukar nauyin bakuncin da ya zama mana tilasta na mutanen da ke yin hijira daga kasashen Nijar ko Chadi ne abin da zai dame mu ba, ya kamata mu nuna damuwarmu ga yiwuwar fadawa halin da makwabatanmu ke ciki, wadanda yunwa ke kokarin ganin bayansu. Rashin faduwar damina da wuri, abu ne da ya zama jiki a wadansu jihohin kasar nan, kamar jihar Kebbi da Sakkwato da Zamfara da kuma wadansu garuruwan da ke makwabataka da kasashen Nijar da Chadi, haka kuma kwararowar hamada na addabar jihar Jigawa da Yobe da Katsina da sauran wadansu jihohin.

A ganin jaridar Aminiya, ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta Nijeriya da na jihohi su yi wani abu game da wannan kalubale na yunwa ta hanyar farfado da madatsun ruwan da aka bar su suka tarwatse a gaba dayan Arewacin kasar nan, wadanda a da ake amfani da su wajen noman rani da kuma samar da ruwan sha. Mafi yawansu a yanzu sun kafe, babu kuma wani kokarin da ya ce a farfado da su. Haka kuma akwai madatsun ruwan da aka fara, amma aka yi watsi da aikinsu, sabo da wadansu dalilai, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yunkura wajen ganin sun kammala su, don a samu halin gudanar da ingantaccen noma a wadannan yankunan.

Har ila yau akwai bukatar gwamnati a kowane mataki ta mai da hankali wajen samar da abubuwan more rayuwa a yankunan karkara, domin a karfafa wa matasa gwiwa don su zauna a garuruwansu, su kuma kama aikin noma gadan-gadan. Tsohuwar dabi'ar nan ta yin kaura daga kauyuka zuwa birane ita ke kara kawo tarnaki ga harkar noma, ganin yadda mafi yawan matasa suke yin banza da noma suke tahowa birane ci-rani, domin samun kaskantattun ayyukan da za su yi. A matsayin Nijeriya na kasar wacce mutanenta ke dogaro da noma, dole ne a daina wannan dabi'a ta ci-rani, domin a kawar da yunwa wacce ke karuwa sakamakon watsi da aikin noma da aka yi.

Jaridar Aminiya ta ce, ya kamata a ce rahoton kungiyar Oxfam ya zama wata matashiya ga gwamnati da kuma sauran jama'a, su tashi tsaye wajen ganin sun yaki tare da kawar da yunwa, idan kuma ba haka ba za mu wayi gari mu samu kanmu a jerin lissafin rahoton wannan kungiya na nan gaba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China