in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen gasar cin kofin kwallon kafa na duniya
2010-07-12 10:54:02 cri

A ran 12 ga wata da sassafe, an yi wasa na karshe ta gasar cin cikin kofin kwallon kafa na duniya a karo na 19 a kasar Afrika ta kudu, kasar Spain ta lallasa kasar Holland da ci daya mai ban haushi, sai ta lashe gasar kofin duniya. Bayan haka, an kawo karshen gasar da aka yi cikin tsawon kwanaki 32 da suka gabata, kuma an daina kallon gasa da aka yi a cikin wata daya da 'yan kwanaki a kasar Sin.

Gasar ta jawo hankulan Sinawa sama da miliyan dari dake son kallon wasan kwallon kafa. A cikin watan da ya wuce, Sinawa da yawa dake son kallon wasan kwallon kafa sun tsara lokutansu don kallon wasanni, har wasu kamfanoni su ma sun daidaita lokacin yin aiki. Bayan da aka kawo karshen gasar, masanan da abin ya shafa sun tunatar da wadanda suka kalli wasan cewa, kamata ya yi a yi kokarin komawa yadda aka saba da lokacin yin aiki cikin hanzari.

A shekarar bana, gidan talabijin na kasar Sin na CCTV ya watsa dukkan wasanni 64 na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Yawancin Sinawa sun kalli wasanni ta talabijin a gida, sai dai kasar Sin ta zama kasar da ta fi yawan mutanen da suka kalli wasan. Ban da haka kuma, wasu manajojin dakunan shan giya da na cin abinci sun bayyana cewa, yawan kudin da suka samu a lokacin gasar ya karu da kashi 50 cikin dari.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China