in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da wani biki a rumfar kasar Afirka ta kudu don murnar kammala gasar cin kofin duniya
2010-07-12 09:16:56 cri

A ran 12 ga wata da sassafe, agogon Beijing, an kammala gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010 a kasar Afirka ta kudu. Kana a ran 11 ga wata da dare, an gudanar da wani biki a rumfar kasar Afirka ta kudu don murnar kammala gasar. A bikin, masu raye-raye na kasar Sin sun yi rawar gargajiya ta kasar Afirka ta kudu, kana masu kallo sun hura vuvuzela. Babban direktan kasar Afirka ta kudu dake birnin Shanghai kuma babban wakilin rumfar kasar Afirka ta kudu Vika Khumalo ya halarci bikin.

Mr Khumalo ya bayyana cewa, kasar Afirka ta kudu ta jawo hankalin duniya domin gudanar da gasar cin kofin duniya, da kasancewa wata kasa ta duniya, kuma dukkan duniya ta kara sanin kasar Afirka ta kudu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China