in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jacques Rogge ya yaba wa gasar cin kofin duniya da ke gudana a Afirka ta Kudu
2010-07-11 16:19:08 cri
Ran 10 ga wata, Jacques Rogge, shugaban kwamitin harkokin wasannin Olympic na kasa da kasa wato IOC ya nuna cewa, gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da ke gudana a kasar Afirka ta Kudu ta sami nasara sosai.

A wannan rana, Mr. Rogge da Jacob Zuma, shugaban kasar Afirka ta Kudu sun yi ganawa. A yayin taron manema labaru da aka yi bayan ganawar, Rogge ya yi wa kafofin yada labaru bayani da cewa, ba za a manta da gasar cin kofin duniya ta Afirka ta Kudu ba, wadda kasaitacciyar gasa ce da dukkan jama'ar Afirka za su yi alfahari da ita. Zuma kuma ya nuna wa kwamitin IOC godiya bisa taimakon da yake ba kasarsa wajen yaki da wariyar al'umma.

Amma Rogge da Zuma dukkansu ba su ce kome ba kan ko Afirka ta Kudu za ta nemi samun bakuncin shirya gasar wasan Olympic bayan ta sami nasarar shirya gasar cin kofin duniya. Kafin wannan kuma, an ce, watakila birnin Capetown ko birnin Durban zai nemi bakuncin shirya gasar wasan Olympic ta shekarar 2020, sa'an nan Rogge ya taba karfafa gwiwar kasashen Afirka wajen neman shirya gasar. A yayin shawarwarin da ke tsakaninsa da kungiyar harkokin wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA a farkon wannan wata, Zuma ya taba bayyana cewa, a ganin Afirka ta Kudu, babu dalilin da ya sa Afirka ta Kudu ba ta nemi samun bakuncin shirya gasar wasan Olympic ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China