in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamus ta samu matsayi na uku a gasar cin kofin duniya ta Afirka ta Kudu
2010-07-11 15:57:02 cri
Ran 10 ga wata da dare agogon kasar Afirka ta Kudu, a cikin karawar da aka yi na neman matsayi na uku a gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da ke gudana a kasar, kasar Jamus ta doke kasar Uruguay da ci 3 da 2.

Kasashen 2 sun nuna sakin jiki sosai kuma sun yi ta kai wa juna hare-hare. Thomas Mueller na Jamus ya fara buga kwallo cikin ragar Uruguay da fara wasan, amma daga baya Edinson Cavani da Diego Forlan na Uruguay sun rama kwallaye daya bayan daya. Duk da haka, Marcell Jansen na Jamus ya rama kwallo, sannan kuma abokin kungiyarsa Sami Khedira ya sake kara buga kwallo a ragar Uruguay, ta haka Jamus ta lallasa Uruguay da ci 3 da 2, ta zama ta uku a gasar cin kofin duniya, wadda karon farko ce ake yi a nahiyar Afirka. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China