in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude ranar dakin nune-nune na kasar Sudan a bikin baje kolin duniya a Shanghai
2010-07-11 15:30:26 cri
A ran 11 ga wata, an bude ranar dakin nune-nune na kasar Sudan a bikin baje kolin duniya a birnin Shanghai. Ministan kula da harkokin yin cinikayya da kasashen waje na kasar Sudan Elisa Nyamlell Wakoson, da mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin kan bikin baje kolin duniya a Shanghai Wu Jiuhong sun halarci bikin tare da yin jawabi.

A cikin jawabinsa, Elisa Nyamlell Wakoson ya bayyana cewa, taken dakin kasar Sudan shi ne "Birane da zaman lafiya", wanda ya bayyana cewa, zaman lafiya na da muhimmanci kwarai da gaske ga kasar Sudan, jama'ar kasar suna hadin kansu wajen kokarin kafa wata kasar mai dawamammen bunkasuwa, da fatan samun wata kyakkyawar makoma a nan gaba. Yayin da yake tabo maganar dangantaka tsakanin Sudan da Sin, Wakoson ya furta cewa, (1)

"Bisa babban taimakon da kuka bayar, dakin nune-nune na nahiyar Afirka cikin hadin kai na jawo hankalin masu sha'awar kallo da yawa daga kasar Sin da ma duniya baki daya, kuma ya yi babbar nasara. Kasar Sin tana da dogon tarihi, tattalin arzikin kasar yana bunkasa yadda ya kamata. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Sin ta ba da gudummawa sosai ga samun bunkasuwar kasar Sudan. Ina fatan a nan gaba kasar Sin za ta kara gabatar da fasahohi masu kyau a Sudan da ma Afirka, har ma a duniya baki daya."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China