in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka ziyarci babban dakin kasashen Afirka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai ya kai miliyan 7 da dubu 500
2010-07-09 21:04:48 cri

Yau 9 ga watan Yuli, Mr. Chen Jintian wanda ke kula da aikin tafiyar da babban dakin kasashen Afirka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai ya fayyace cewa, ya zuwa yau, yawan mutanen da suka kai ziyara wannan babban dakin kasashen Afirka ya kai fiye da miliyan 7 da dubu dari 5. Kuma an yi hasashen cewa, ya zuwa karshen watan da muke ciki, yawan mutane da za su kai ziyara babban dakin kasashen Afirka zai kai fiye da miliyan 10.

Mr. Chen Jintian ya bayyana cewa, bayan da aka bude kofar farfajiyar bikin EXPO na Shanghai a ran 1 ga watan Mayu, dimbin masu yawon bude ido sun kai ziyara babban dakin kasashen Afirka. Haka kuma, a ran 28 ga watan Mayu, yawan mutanen da suka kai ziyara wannan babban dakin kasashen Afirka ya kai fiye da miliyan 1. Sakamakon haka, yau da maraice, agogon Beijing, babban dakin kasashen Afirka zai jawo mai yawon bude ido na miliyan 7 da dubu dari 5. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan mutanen da suka kai ziyara babban dakin kasashen Afirka ya kai kashi 30 cikin dari bisa na jimillar mutanen da suka kai ziyara a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai.

Mr. Chen ya kara da cewa, wannan ya kasance tamkar wani babban daki ne mai zaman kansa, kuma yawan mutanen da suka ziyarci dakin ya fi na sauran dakunan kasa da kasa yawa, kuma wannan ya alamta cewa, babban dakin kasashen Afirka yana jawo hankalin masu yawon bude ido sosai. Bisa shirin da aka tsara, yawan mutanen da babban dakin kasashen Afirka zai iya karba ya kamata ya kai dubu 50 a kowace rana, amma a hakika dai, yanzu matsakaicin yawan mutanen da suka kai ziyara a wannan babban daki ya kai dubu 130 a kowace rana, har ma wannan adadi ya taba kai dubu 180 a yini guda.

Fadin babban dakin kasashen Afirka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai ya kai fiye da murabba'in mita dubu 270, inda ke kunshe da kananan rumfunan kasashen Afirka 42 da wata rumfar kungiyar AU. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China