in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na kungiyar kasashe takwas masu ci gaban addinin musulunci ya yi kira ga karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya
2010-07-09 09:22:07 cri

A ran 8 ga wata, a Abuja, babban birnin kasar Najeriya, an kawo karshen taron koli na kungiyar kasashe 8 masu ci gaban addinin musulunci a karo na 7. A gun taron, an zartas da "Sanarwar Abuja ta shekarar 2010", wadda ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su kara hadin gwiwa a fannonin zuba jari da tattalin arziki da cinikayya.

Sanarwar ta ce, a halin yanzu, yawan jarin da kasashen takwas ke zubawa juna bai kai karfinsu ba. Kasashen takwas sun sake nanata daukar tsararrun matakai na sa kaimi kan kasashe waje da su zuba jari kai tsaye a fannonin da abin ya shafa. A sa'I daya kuma, kasashen takwas suna nuna goyon baya ga hadin gwiwa a tsakanin kanana da matsakaitan kamfanoni.

Bugu da kari, kasashen sun amince da karfafa hadin kai a fannonin raya kasa, sayar da fasahohi, bunkasa sabbin makamashi da yin amfani da makamashin nukiliya da sauransu.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China