in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin murnar ranar rumfar kasar Ghana a cikin farfajiyar bikin EXPO
2010-07-08 16:23:04 cri

A ranar 8 ga wata, an yi bikin murnar ranar rumfar kasar Ghana a farfajiyar bikin EXPO da ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin.

Manyan jami'an da suka halarci bikin sun hada da Madam Hanna Tetteh, minista mai kula da cinikayya da masana'antu ta kasar Ghana, da Jiang Zhengyun, mataimakin babban kwamishinan gwamnatin kasar Sin mai kula da bikin baje kolin duniya na EXPO. Bayan da jami'an suka jinjina wa tutar kasar Ghana, sun shiga cikin babban daki mai taken 'cibiyar EXPO' inda suka fara ba da jawabi.

Cikin jawabinsa, Mista Jiang Zhengyun ya nuna yabo kan hulda mai kyau da aka kulla a tsakanin kasashen 2, kamar yadda ya fadi cewa, shekarar bana ta kasance shekara ta 50 bayan da Sin da Ghana suka kulla huldar diplomasiyya. Sa'an nan a cikin wadannan shekaru da suka wuce, bangarorin biyu sun yi ta kokarin hadin kai da juna, da nuna wa juna amincewa, tare da neman kyautata huldar da ke tsakaninsu zuwa sabon matsayi. Bayan haka kuma, a nan gaba gwamnatin Sin za ta ci gaba da kokarin da take yi wajen yin hadin gwiwa da kasar Ghana.

A nata bangaren kuma, Madam Hanna Tetteh, a madadin gwamnatin kasar Ghana da jama'arta, ta nuna godiya ga kasar Sin dangane da goyon bayan da take baiwa kasar Ghana, inda ta yi bayani kamar haka,kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashen ketare wadanda suka fi zuba jari a kasar Ghana, abin da ya amfana wa jama'ar kasar sosai. Sa'an nan kasar Ghana za ta yi amfani da EXPO don neman habaka hadinkan kasashen biyu, da kuma kyautata wani tsarin raya tattalin arziki tare da kiyaye muhalli. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China