in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a tabbatar da wanda zai mika kofin duniya na gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ba
2010-07-08 08:55:51 cri
Yau ya rage sauran kwanaki 4 a kaddamar da gasar karshe ta gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya, amma har yanzu hukumar FIFA ba ta tabbatar da wanda zai mika kofin duniya ba.

Idan tsohon shugaban kasar Mandela zai halarci gasar karshen da za a gudanar a filin wasan kwallon kafa mai suna FNB, mai yiyuwa ya mika kofin duniya ga kungiyar da ta zama zakara. Amma bisa labarin da kakakin hukumar FIFA ya bayar, an ce, ba a tabbatar da Mandela zai halarci gasar karshen ba.

A cikin wata sanarwa da asusun Mandela ya bayar, an tabbatar da cewa, Mandela ya riga ya sami takardar gayyatar da hukumar FIFA ta bayar, amma Mandela zai yanke shawarar ko zai halarci gasar karshe a ran da za a gudanar da gasar.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China