in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta halarci bikin EXPO na Shanghai tare da samun karuwa, in ji mai rumfar kasar
2010-07-09 20:36:42 cri
Ranar 8 ga watan Yuli ta kasance ranar rumfar kasar Ghana da ke farfajiyar bikin EXPO, ranar da wasu manyan jami'an kasar tare da wasu jami'an kasar Sin suka halarci wani biki na musamman da aka shirya a wajen babban gini mai taken 'cibiyar EXPO' da ke cikin farfajiyar bikin EXPO, inda masu fasahohi na kasar Ghana suka nuna fasahohinsu don murnar ranar da kuma kayatar da jama'a. Sa'an nan don neman sanin yadda kasar Ghana ta shirya domin biki na EXPO, na yi hira da Madam Stella Ansah, jami'ar da ke kula da rumfar kasar,wadda ta yi bayani kan babban taken rumfar kasar kamar haka,

'Ghana ta halarci bikin EXPO bisa babban jigonta na 'biranen da suka zama tamkar ni'imtattun wurare'.Mun tabbatar da jigon ne domin muna neman raya biranenmu zuwa wurare masu ni'ima, inda za a samu bishiyoyi da wurin shakatawa. Mutane za su iya hutawa a wajen, tare da yin wasa da kayan kida, su kuma taka rawa. Ka san mutanenmu na son buga ganguna da taka rawa sosai.'

Madam Stella Ansah ta ce, a wajen rumfar kasar Ghana, ana kokarin baje kolin wasu abubuwa wadanda a kasar Ghana kadai ake iya samunsu, kamar gidajen gargajiya na arewacin kasar, da babbar kofa mai nuna 'yancin kan kasa da aka gina ta a birnin Accra, da wasu kayayyakin aikin hannu, da yadda kasar Ghana take da dimbin albarkarun da Allah ya hore mata. Sa'an nan, an baje kayayyakin da aka samu ta hanyar sarrafa koko, wanda ya kasance daya daga cikin muhimman kayayyakin da kasar ke samarwa. Ban da haka kuma cikin abubuwan da ake nunawa akwai sakakkan kaya na musamman da aka saka a kasar Ghana mai taken 'Kenti', kayan da aka san jama'ar kasar Ghana dasu,wanda ya sa ake iya bambanta mutanen kasar Ghana daga sauran al'ummomin Afirka.

Ban da wannan kuma, yadda jama'ar kasar Sin suke nuna sha'awa kan abubuwan da kasar Ghana ke baje koli a cikin rumfarta ya sanya Madam Ansah gamsuwa, kamar yadda ta fadi cewa,

'Na tabbata za ka iya ganin yadda mutane suke tsayawa a cikin dogon layi domin jiran shiga rumfarmu, domin suna da sha'awa sosai game da abubuwan da muke nunawa a nan. Sun kalli zane-zanenmu, sa'an nan sun taba tufafin da muke nunawa da hannu, abubuwan da suka burge su sosai. Za su so su kara sanin kasar Ghana: A ina take? Me ya sa kasar take da fitattun 'yan wasan kwallon kafa da yawa? Hakan zai ba mu damar kara fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasar Ghana.'

Sa'an nan, game da ma'anar da ake da ita wajen shirya bikin baje kolin duniya, Madam Ansah ta ce, EXPO din ya zama wani dandali mai kyau inda mutanen duniya za su hadu domin musanya ra'ayoyi, da fasahohi. Sa'an nan ta nuna imani kan kasar Ghana za ta karu da abubuwa da dama bisa halartar bakin baje kolin duniya, kamar yadda ta bayyana cewa,

"Za mu amfana sosai, domin kamar yadda na gaya maka kasarmu na da albarkatu da yawa, shi ya sa muna neman yin amfani da bikin EXPO din domin janyo mutanen da za su zuba jari a kasarmu, ta yadda za a iya kara samar da ayyukan yi ga jama'ar kasar. Hakan zai ba jama'ar kasarmu damar kara samun kudin shiga, daga baya kuma za a samun kyautatuwa dangane da zaman rayuwarsu." (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China