in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lardin da kankara da dusarta suka bambanta shi da saura a kasar Sin
2010-07-07 15:38:06 cri

Hausawa kan ce Allah daya gari bamban. Wannan ya yi daidai da yadda Allah ya yalwata kasar Sin da fadin kasa, wadda ta karkasu zuwa larduna da yankuna, har ma zuwa garuruwa da unguwanni. Dan haka ya dace a fahimci wani muhimmin al'amari game da hakan, na cewa a irin wadannan sassa na kasar ta Sin akwai al'ummu masu al'adu daban-daban, kamar yadda yanayin muhallansu suke.

Lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin Sin mai Harbin a matsayin babban birni, daya ne daga cikin lardunan kasar. Lardi ne mai fadin murabba'in 454,000 sq. Kuma adadin yawan jama'arsa ya kai miliyan 36.89, kamar yadda wata kididdiga da aka yi a shekara ta 2000 ta nuna. Yanayin lardin ya samar masa yawan saukar kankara da dusarta sakamakon tsananin sanyi da yake da shi. Hakan ya sa ake yiwa lardin kirari da "Lardin da kankara da dusarta suka bambanta shi da saura".

A kokarin nuna yadda wannan lardi na Heilongjiang ya ke alfahari da yanayin da Allah ya arzuta shi da shi ne, a ranar Talata bakwai ga watan Yuni ya kaddamar da makonsa a bikin baje kolin kasa da kasa da ke gudana a birnin Shanghai na kudancin Sin. Bikin kaddamarwar da aka yi a dakin taro na cibiyar yada labarai ta kasa da kasa da ke cikin farafajiyar baje kolin, ya samu halartar wasu jiga-jigan mutane daga lardin kamar Sun Yao mataimakin gwamna da Du Jia Hao wanda shi ma mataimakin gwamnan lardin na Heilongjiang ne. Ko baya ga jami'an gwamnatin akwai wasu fitattun 'yan wasan kasar Sin 'yan asalin lardin kamar su Yang Yang, Wang Meng, Shen Xue da Zhao Hongbo da dai sauransu. Sai kuma wasu kungiyoyin jama'a masu asali daga lardin da suka halarci wajen don nuna goyon bayansu.

Mr. Sun Yao mataimakin gwamnan lardin Heilongjiang, a yayin kaddamar da makon ya gabatar da wani jawabi dangane muhimmancin da lardin ke da shi ga kasar Sin ta fannonin tattalin arziki, siyasa da zamantakewar al'umma. A jawabin nasa Mr. Sun ya ce lardin Heilongjiang yana da kasar noma mafi girma a Sin, kana wajen da ya fi samar da kayan abinci dangin hatsi a sakamakon yalwar kasar noma a lardin. Ya ce yawan adadin muhimman kayan abinci kamar su shinkafa, waken soya da masara da sauran kayan abinci dangin hatsi da lardin ke samar wa a tsawon shekara kan kasance a sahun gaba a duk kasar ta Sin.

Mr. Sun Yao ya kara da cewa, a matsayin lardin farko da ya samu ikon tafiyar da harkokin kansa a jamhuriyar jama'ar Sin, ya kasance daya daga cikin jiga-jigan matattarar masana'antu. Inda Heilongjiang ke kasancewa mai mallakar tabbatattun turakun kafa masana'antu da suka kunshi makamashi, danyu ko kayan hada wasu kayayyakin, da kuma sinadaran da suka shafi albarkatun man fetur.Yankin ya na da albarkatun karkashin kasa, kamar kwal wanda mahakarsa da ke a gabashin Heilongjiang din take samar da kashi daya bisa goma na baki dayan adadin kwal din da Sin ta kan samar. Sai kuma man fetur wanda in an yi zancensa abu na farko da za a tuna a lardin shi ne sararin man fetur na Daqing, wanda ba tare da wani cikas ba a tsawon shekaru goma nan gaba ake saka ran ya dinga samar da tan miliyan arba'in a duk shekara.

Wani karin haske da Mr. Sun Yao ya yi shi ne na yadda lardin Heilongjiang ya zama mafi girma a kasar Sin wajen gudanar da harkokin hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki, cinikayya, kimiyya da fasaha tsakanin Sin da kasar Rasha. Kana tsawon shatin kan iyaka a tsakanin Rasha da Heilongjiang ya kai kilomita 3,038, wanda ke da fitattun tasoshin ruwa na doron kasa guda ashirin da biyar, da wasu yankunan cinikayyar hadin gwiwa a kogunan Heihe, Suifenhe da Dongning.

Lardin Heilongjiang dai ya kasance mai dogon tarihi da nagartattun al'adu. Akwai dai shedar da ke nuna wanzuwar wasu ayyuka da bil Adama suka gudanar a da can, wajen tsawon shekaru dubu talatin zuwa arba'in. Wato lokacin dauloloin da suka gabaci daular Qin. Daga lardin Heilongjiang ne dai kasar Sin ta fara yakin nuna kiyayya da mamayar Japan, kana lardin ne ya sheda fafatawar karshe ta yakin duniya na biyu.

Game da masu son yin yawon shakatawa kuwa, lallai lardin Heilongjiang waje ne da ba za a dauke kai gare shi ba. Waje ne da yake da albarkatun gandun daji da yawan kankara da dusarta wadanda a yanzu har ma sun kasance a kan sassaka su bada wasu alamu, kana har ma ana iya gudanar da wasanni a kai. Ga misali bikin kasa da kasa na kankara na Harbin daya ne daga cikin bukukuwa hudu irinsa da ake yin sauran ukun a kasashen Norway, Japan da Canada. Akwai kuma wasu wuraren shakatawa na kawa.

Hausawa dai kan ce "gani ya kori ji", dan haka ne mahukuntan yankin suke ci gaba da shelanta yin ficen da lardin ya yi ta fuskoki da dama a bikin baje kolin kasa da kasa da ke gudana a birnin Shanghai, wadanda kuma ba mai yiwuwa ba ne a dan karamin lokacin da muke da shi a nan ya ishe mu bayyanawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China