in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Holand ta shiga gasa ta karshe ta cikin kofin duniya
2010-07-07 11:09:21 cri

A cikin gasar kusa da ta karshe ta cin kofin duniya da aka yi a ran 6 ga wata, Holamd ta lashe Uruguay da 3-2 haka ya ba ta damar shiga gasa ta karshe ta cikin kofin duniya bayan shekaru 32.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci, bi da bi ne dan wasa Giovanni Vanbronckhorst na Holand da dan wasa Diego Forlan na Uruguay sun jefa kwallo raga ta hanyar bugun nisa gola. An je hutun rabin lokaci da 1-1. Bayan an dawo daga hutu, dan wasa Rafael Van der Vaart na Holand ya yi shigar, sai bi da bi ne dan wasa Wesley Sneijder da Arjen Robben na Holand suka ci kwallo daya daya. A karin lokaci, dan wasa Maxi Pereira na Uruguay ya ci daya. Ko da yake alkalin wasa ya ba da karin lokaci mintoci 5, duk da haka Holand ta lashe Uruguay da 3-2. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China