in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya dage haramcin da aka yiwa kungiyar kwallon kafa ta kasar
2010-07-06 20:17:45 cri

A ran 5 ga wata, kakakin shugaban kasar Nijeriya Ima Niboro ya bayyana cewa, shugaban kasar Goodluck Jonathan ya dage haramcin da aka yiwa kungiyar kwallon kafa ta kasar na tsawon shekaru 2.

Mr Ima ya bayyana cewa, shugaba Jonathan ya yanke shawarar ce bayan da ya gana da jami'in hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar da ministan harkokin wasanni na kasar. A ganawar, wani jami'in hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar ya nemi gafara daga shugaba kasar da jama'arta domin gazawar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Afirka ta kudu, kana ya sanar wa shugaban kasar kudurin wargaza kungiyar. Kana ya yi alkawari cewa, kawar da tsohon shugaban hukumar daga kujerarsa shi ne mataki na farko dangane da kwaskwarimar da ake kan tsarin wasan kwallon kafa a kasar, ta yadda za a inganta sha'anin wasan kwallon kafa a kasar yadda ya kamata. Kazalika ya bayyana cewa, zai dauki alhakin da shugaban kasar da jama'arta suka dauka masa tare, da sake kafa sabuwar kungiyar wasan kwallon kafa a kasar, da kuma sake dawo da mutuncin kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar a idon duniya.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China