in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya kawar da haramcin da ya dora kan kungiyar kwallon kafa ta kasar
2010-07-06 14:30:20 cri
Biyo bayan wata ganawar sirri a tsakanin shugaba Goodluck Jonthan na Najeriya da hukumar kula da harkokin wasannin kwallon kafa ta kasar NFF, a fadar shugaban ranar Litinin din nan ne gwamnatin kasar ta yanke shawarar sauya ra'ayi game da matakin hana kungiyar kwallon kafa ta kasar da aka fi sani da super eagles, shiga duk wani wasa a matakin kasa da kasa na tsawon shekaru biyu.

Ta cikin wata sanarwa da Ima Niboro, mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya fitar, an bayyana cewar gwamnatin Najeriyar ta yanke shawarar yin hakan ne sakamakon tabbacin da ta samu daga hukumar ta NFF, na aiwatar da wani kasaitaccen shirin bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa a kasar.

A yayin ganawar hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta nemi afuwar shugaban da sauran jama'ar kasar, kan rashin tabuka wani abu a bangaren 'yan wasan kungiyar super eagles a gasar cin kofin duniya da yanzu haka ake gab da kammalawa a kasar Afirka ta kudu. Kana hukumar ta sanar da shugaban kan kudurinta na wargaza kungiyar, tare da yin garambawul a fannonin da suka dace wajen kula da harkokin kwallon kafa a Najeriya.

Sanarwar ta kara da bada tabbacin hukumar na bullo da shirin bunkasa harkokin kwallon kafa mai dorewa, gami da kafa wata sabuwar kungiyar zaratan 'yan wasa a ajin manya da zata farfado da sunan kasar, maimakon ci gaba da kunyatata a wannan fage. Sannan mahukuntan NFF din sun sanarwa da shugaban cewa, farawa da bisimilla, sun kuduri aniyar yin gyara a kansu, inda suka kawar da tsohon shugaban hukumar Sani Lulu daga kujerarsa a karshen makon da ya gabata saboda gazawar kungiyar super eagles a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Afirka ta kudu. bana. Tsigewar dai bata tsaya kansa shi daya ba, ta ma shafi wasu gigga sha uku na hukumar ta NFF, da suka hada da Mataimakin shugaban Amanze Uchegbulam, da Taiwo Ogunjobi shugaban kwamitin kula da bada horo.

Sakamakon wannan tabbaci, gami da roko daga sassan al'ummar Najeriya ne ciki har da tsoffin shugabanninta, shugaba Jonathan ya yanke shawarar sake bibiyar haramcin da ya dorawa kungiyar a baya na shekaru biyu ba tare da halartar wasannin kasa da kasa ba. Kana Ima Niboro ya ce wannan sauyin tunani zai baiwa sauran 'yan wasa a matakai daban-daban na Najeriya damar halartar gasannin kwallon kafa a duniya, a yayin da ake ci gaba da kokarin kafa wata sabuwar babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa.

Niboro ya kuma ce, shugaban kasar ya umarci ministan kula da harkokin wasanni, kan ya kira taron masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa don farfado da cibiyoyin horas da wasan, da ma duk wata kafa ta zakulo zaratan 'yan wasa, don fito da sabbin jinin madaka tamaula, da ma sauran masu kasancewa cikin wasanni daban-daban, don ci gaban kasar. A baya dai fadar shugaban ta bayyana cewa wannan haramci na da nufin samar da damar yin gyara don tinkarar kalubalolin kasa da kasa a fagen wasan kwallon kafa. Har ila yau Jonathan, ya yi umarni kan a gudanar da sahihin bincike game da adadin kudin da aka yi amfani da shi, don halartar gasar ta cin kofin duniya, tare da fitowa fili wajen neman gano ko akwai wata badakala a harkar.

Ita dai hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta dauki matakin gwamnatin Najeriyar ne a matsayin kutsen siyasa, wajen kula da harkokin kwallon kafa, kana ta baiwa gwamnatin Najeiyar wa'adin zuwa karfe shida agogon GMT na maraicen ranar Litinin don sauya matsayinta ko kuwa ta dakatar da kasar daga duk wata harkar da ta shafi kwallon kafar kasa da kasa. Har ma FIFA din ta dan bada haske na fara shirin gayyatar wata kasa da zata maye gurbin Najeriya a gasar mata 'yan kasa da shekaru ashirin da za a yi nan gaba a kasar jamus.(Garba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China