in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xin Jiang ta kara samun kudin shiga daga yawon shakatawa
2010-07-05 21:02:47 cri

A kwanakin baya, Inam Naisilting shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa ta jihar Xinjiang ta Uighur mai cin gashin kanta ya nuna cewa, a farkon rabin shekarar 2010, yawan mutane masu yawon shakatawa daga gida da ketare da aka karba ya kai miliyan 10, wannan ya karu da kashi 9 cikin kashi 100 bisa na shekarar 2009, kuma yawan kudin da aka samu daga yawon shakatawa ya kai RMB yuan biliyan 10.2, wannan ya karu da kashi 10 cikin kashi 100 bisa na shekarar 2009.

Inam ya fayyace haka ne a taron fadin albarkacin baki da aka yi kan aikin bunkasa yawon shakatawa a yankin Xinjiang na shekarar 2010. bisa labarin da muka samu, an ce, bisa shirin bunkasa yawon shakatawa na yankin Xinjiang da aka yi, ya zuwa shekarar 2015, yawan kudin da za a samu daga yawon shakatawa a yankin Xinjiang zai kai RMB yuan miliyan 70. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China