in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xinjiang, wani dandali ne na kabilu daban daban
2010-07-05 20:37:17 cri

Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin, kuma tana da iyaka da kasashe takwas, ciki har da Rasha da Kazakhstan da Kyrghizstan da Tajikistan da Pakistan da Mongoliya da Indiya da kuma Afghanistan. Fadin jihar Xinjiang ya kai muraba'in kilomita miliyan 1 da dubu 660, wanda ya kai kashi daya daga cikin kashi shida na fadin kasar Sin baki daya, abin kuma da ya sanya jihar a matsayin jiha mafi fadi a kasar Sin. Xinjiang tana da wadatar albarkatun kasa iri iri, ciki har da koguna da tabkoki da halittu da kuma ma'adinai. Xinjiang wuri ne mai ni'ima, sabo da haka, ta shahara sosai wajen yawon shakatawa. Yawan mutanen Xinjiang ya kai miliyan 20 da dubu 951, kuma daga cikinsu, kashi 60.7% sun kasance 'yan kananan kabilu. Tun zamanin da, Xinjiang wuri ne da kabilu da dama ke zaman cude-ni-in-cude-ka, kuma yanzu haka jihar Xinjiang tana da kabilu da dama da yawansu ya kai 47, musamman ma kabilu 13 wadanda suka fara zama a jihar ta Xinjiang tun kaka da kakanninsu, ciki har da Uygur da Han da Kazak da Hui da Khalkhas da Mongoliya da Tajik da Xibe da Man da Uzbek da Rasha da kuma Tartar.

To, yanzu bari in zagaya da ku zuwa wasu birane a jihar Xinjiang.

Korla wani birni ne da ke tsakiyar jihar Xinjiang, inda 'yan kananan kabilu 23 ke zaman rayuwarsu, ciki har da Uygur da Mongoliya da Kazak da sauransu. Birni ne mai ni'ima, kuma ya shahara sosai da 'ya'yan itatuwan da ake kira pear.

Aler Mahiptr, dan shekaru 15 da haihuwa, yana karatu a wata makarantar sakandare da ke birnin Korla, ya ce mana, ko da yake yana karatu cikin wata makarantar 'yan kabilar Uygur, amma yana da dimbin abokai 'yan kabilar Han, kuma ya kan yi wasa da su. Ya ce,"Mu kan je wurin shan iska tare da abokanmu na kabilar Han, kuma mu kan yi wasannin internet tare. Iyayena ma suna da abokai cikin kabilar Han, kuma sun shaku da su sosai. Da na girma, zan bude wani babban kanti tare da abokaina na kabilar Han, mun dauki alkawari."

Mazauna birnin Korla na kabilu daban daban suna son garinsu tare da yin alfahari da shi. Duk da haka, yau da shekaru 30 da suka gabata, fako ne kawai aka gani a Korla, wanda kuma yake da nisan kilomita 70 daga hamadar Takla Makan, hamadar da ta zo ta biyu daga cikin manyan hamadun duniya.

Domin kyautata yanayin wurin, gwamnatin Korla ta gabatar da manufar mayar da Korla ya zama wani kore. Tun daga shekarar 1997, ta fara gwaje-gwajen dasa bishiyoyi, kuma a shekarar 1999, ta shigar da fasahar zamani daga Isra'ila, wadda ake ban ruwa ga bishiyoyi ba tare da ruwa da yawa ba. Kawo yanzu dai, an dasa bishiyoyi a duwatsu da fadinsu ya kai kadada dubu hudu a garin, aikin da aka kashe kudin Sin miliyan 108.

Ashamjam Gariti, magajin garin Korla ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun baya, ba ma kawai an mai da hankali a kan kyautata muhalli, haka ma an gudanar da jerin harkokin al'adu, wadanda suka kyautata zaman rayuwar al'umma ta fannin al'adu. 'Yan kabilu daban daban da ke zama a Korla sun kasance 'yan uwa a yayin da suke gina garinsu, abin kuma ya samar da sabon kuzari ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a birnin Korla. Ashamjam Gariti ya ce,"Yawan GDP ya kai kudin Sin yuan miliyan 100 a Korla a shekarar 1979, kuma matsakaicin kudin shiga na manoma ya kai yuan 75. Amma ya zuwa shekarar 2008, yawan GDP namu ya kai yuan biliyan 43, a yayin da kudin shiga na kowane manomi ya karu har zuwa yuan 6660."

To, masu sauraro, bayan da muka zagaya da ku birnin Korla, bari mu je birnin Kashkar da ke jihar Xinjiang, wanda kuma ya fi kasancewa a yammacin kasar Sin. Kashkar ya dade, kuma al'adunsa sun bunkasa sosai. Duk da haka, akwai dimbin lalatattun gidaje cikin tsohon garin Kashkar sakamakon dadadden tarihin garin, kuma akasarin gidajen da aka gina da katako ba su iya tinkarar girgizar kasa.

Tun shekarar 2008, domin kiyaye mazauna garin da kuma ba da kariya ga kayayyakin tarihi, gwamnatin garin ta fara gyaran tsohon garin. Kawo yanzu, iyalai 580 sun kaura cikin sabbin gidajen da aka gina wadanda ke iya tinkarar girgizar kasa.

Mrimurti Jam, wanda ke da shekaru 9 da haihuwa, ya ce, iyalansa sun shiga sabon gida ba da jimawa ba. Kamar yadda ya ce,"bubu bayan gida cikin tsohon gidanmu, amma ga shi akwai shi cikin sabon gida. Kuma tsohon gida karami ne, amma sabon gida na da girma. Yanzu muna jin dadin zamanmu."

A yayin da Dawti Mathirsuti, wanda ke da shekaru fiye da 80 a duniya, wanda ya gane wa idonsa bunkasuwar jihar Xinjiang, ya ce,"yanzu muna da gida mai kyau, zaman rayuwarmu ya kyautata, akwai albarka da kwanciyar hankali, kuma kowa na jin dadin zama, kabilu daban daban sun kasance tamkar 'yan uwa ne. musamman bayan da aka fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, an sami manyan sauye-sauye a jihar Xinjiang, kuma sauye-sauyen sun faru ne a sanadiyyar kyakkyawan jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma hadin kan kabilu daban daban."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China