in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta za bayar da RMB fiye da biliyan 680 kan sabbin ayyuka 23 game da manufar bunkasuwar yankunan da ke yammacin kasar
2010-07-05 18:30:28 cri

Wakilinmu ya samu labari daga kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin a ranar 5 cewa, gwamnatin kasar Sin za ta bayar da kudin Sin RMB fiye da biliyan 680 kan sabbin ayyuka 23 game da manufar bunkasuwar yankunan da ke yammacin kasar.

Wadannan sabbin ayyuka sun kunshi gina filin jiragen sama masu cin gajeren zango a yankunan dake yammacin kasar Sin, da tashar samar da wutar lantarki, da sauransu. Ya zuwa shekarar 2009, yawan sabbin ayyuka da kasar Sin ta gudanar game da manufar bunkasuwar yankunan da ke yammacin kasar ya kai 120, jimilar kudin da aka ware kan ayyukan kuma ya kai kudin Sin RMB biliyan 2200. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China