in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan tallafawa jihar Xinjiang za su taimaka ci gaban tattalin arzikin jihar
2010-07-05 17:53:12 cri
Ranar 5 ga wata, rana ce ta cika shekara daya da abkuwar tashe-tashen hankali a birnin Urumqi na jihar Xinjiang wanda ya faru a ranar 5 ga watan Yulin shekara ta 2009. A halin yanzu a birnin, jama'a sun fi mayar da hankali kan matakan da za'a dauka domin neman ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zaman al'umma a jihar. Kwararru sun bayyana cewa, sakamakon jerin matakan da aka fitar na tallafawa jihar Xinjiang, jama'ar wurin da sauran al'ummar kasar Sin suna yin kokari tare wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman al'umma a Xinjiang.

A yayin taron karawa juna sani da aka yi kwanan baya dangane da ayyukan jihar Xinjiang, gwamnatin kasar Sin ta tsara wasu manyan manufofi da shirye-shirye, a kokarin taimakawa ci gaban jihar, gami da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Xinjiang. Haka kuma, jama'ar Xinjiang suna mayar da hankali sosai kan wadannan kwararan matakan da gwamnatin kasar ta dauka na tallafawa jiharsu, amma bin tambaya shi ne ko za'a iya aiwatar da wadannan matakai yadda ya kamata? Game da wannan batu ne, darektan sashin nazarin tarihin kan iyakokin kasar Sin ta cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar, manazarci Li Sheng yana ganin cewa, a halin yanzu, gwamnatin kasar Sin tana yin matukar kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Xinjiang, inda ya ce:

"Tashin hankalin da ya abku a ranar 5 ga watan Yulin shekara ta 2009, wani lamari ne wanda ba'a taba ganin irinsa ba a cikin tarihin jihar Xinjiang shekaru 100 da suka gabata. Kawo yanzu, ana fuskantar barazana, kuma zaman al'umma bai dawo kamar yadda yake a baya ba. Yanzu abubuwan da jama'ar Xinjiang suka fi bukata su ne, na farko, yanayin tsaro, na biyu kuwa shi ne kwanciyar hankali. A halin yanzu, gwamnatin kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar, gami da 'yan sanda da rundunonin sojoji suna daukar matakai iri-iri domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar."

A game da ayyukan da suka shafi raya jihar Xinjiang, gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, kamata yayi a dukufa ka'in da na'in wajen mayar da ayyukan bada tabbaci da kyautata zaman rayuwar al'umma a gaban kome. A nasa bangaren kuma, manazarci Li Sheng ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mayar da hankali kwarai da gaske kan kyautata zaman rayuwar jama'ar Xinjiang ne domin biyan bukatun jama'ar wurin. Mista Li ya furta cewa:

"Gwamnatin kasar Sin ta kuduri aniyar tallafawa jihar Xinjiang, ta yadda tattalin arzikin jihar, tare da zaman rayuwar jama'ar wurin za su samu bunkasuwa tare kuma yadda ya kamata. Idan ba'a mayar da hankali ko kuma warware matsalolin da suka shafi zaman rayuwar al'umma yadda ya kamata ba, jama'a ba za su gamsu ba."

Bugu da kari, a nata bangaren, mataimakiyar shehun malami daga sashin nazarin ilimin siyasa daga makarantar horas da mahukunta 'yan jam'iyyar kwaminis ta jihar Xinjiang ta Uyghur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, Madam Li Dan ta yi nuni da cewar, matakan da gwamnatin kasar take aiwatarwa a fannonin bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a a Xinjiang, sun samar da ingantaccen tushe ga ci gaban jihar, inda ta ce:

"Ta hanyar yin amfani da tallafin kudin da aka ba mu, ya kamata mu hada ayyukan gina gidajen kwana, da kara samar da kudin shiga ga manoma da makiyaya tare da wasu sana'o'inmu. Idan manoma da makiyaya suka kara samun kudin shiga, to, ko shakka babu, zaman rayuwar jama'ar Xinjiang zai samu kyautatuwa kwarai da gaske."(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China