in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Bafana-Bafana sun daga sunan kasarsu
2010-07-05 09:26:45 cri
Shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya dake gudana a kasar Afirka ta Kudu Danny Jordan ya bayyana cewa, an fitar da 'yan wasan Bafana-Bafana na Afirka ta kudu daga gasar Cin kofin duniya amma sun shiga zukatan dukkan 'yan kasar Afirka ta kudu da ma duniya baki daya a wannan dare bayan wasan kasar na karshe na rukuni-rukuni tsakaninta da kasar Faransa a Mangaung/Bloemfontein.

Ko da yake kasar Afirka ta kudu ta lashe wannan wasa amma ba ta samu makin da ake bukata don kaiwa ga zagaye na gaba na gasar ba.

Ya kara da cewa, "Hakika ba su samu nasarar kaiwa ga zagaye na gaba na gasar ba, amma sun yi abin da kasar ta bukace su su yi, sun yi wasa da kishin kasa da salon taka leda da sadaukar da kai, sun yi bakin kokarinsu. Sun daga martabar rigar kungiyar kasar da kowane dan kasar Afirka ta kudu kuma mana gode musu da irin abin da suka yiwa wannan kasa."

Har ila Jordan ya godewa 'yan kasar Afirka ta kudu bisa ga cikakken goyon bayan da suka nuna wa 'yan wasan na Afirka ta kudu.

Ya ce, "Irin salo da kwazon da muka gani daga kowane lungu da sakon Afirka ta kudu a makonnin nan, ya sa 'yan gida da baki sun ji armashin gasar."

Jordan bai yarda cewa fitar da Afirka ta kudu da aka yi daga gasar za ta shafi baki dayan nasarar gasar ba.

Ya ce, "Gasar ta kare wa 'yan wasan Afirka ta kudu amma ba ta kare wa Afirka ta kudu ba. Har yanzu ana gudanar da gasar a Afirka ta kudu. Ba za mu koma gida ba, ana gudanar da gasar a gidanmu."

Ya bayyana cewa, "Yan Afirka ta kudu sun nuna goyon bayansu ga 'yan wasan Afirka ta kudu. Kuma ba don miliyoyinsu ba da ba mu gina filayen wasa irin na zamani guda 10 ba da bude sabbin filayen jiragen sama da manyan hanyoyi da tashoshin jiragen kasa a wannan lokaci ko kuma karbar dubban daruruwan baki zuwa kasarmu. Da ba mu karbi sama da rabin wasannin gasar cikin nasara ba."

Jordan ya ce, "Ina mai tabbacin cewa, kasar Afirka ta kudu za ta ci gaba da kasancewa mai masaukin baki mai kyau nan zuwa makwanni biyu da rabi masu zuwa kana za ta yi amfani da wannan lokaci a tarihin kasarmu wanda muka yi nasara matuka."

Jordan ya ce, "Goyon bayan da aka baiwa gasar ya zuwa wannan lokaci ya cimma dukkan hasashen da ake inda mutane 1570447 suka kalli wasanni 32 na farko. Sama da mutane miliyan daya ne suka kalli wasannin a filayen wasanni 10 na hukumar FIFA a kasar Afirka ta kudu kuma karin dubban daruruwa sun kalli wasannin a wuraren da aka tanada don kallon irin wadannan wasanni a bainar jama'a a fadin kasar.

Birnin Durban ya kasance a kan gaba, inda hukumar FIFA ta tabbatar da cewa, kimanin baki 238546 ne suka ziyarci birnin daga lokacin da aka fara gasar har zuwa ranar 20 ga watan Yuni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China