A karawar da ya gudana a tsakanin Jamus da Argentina, a minti 3 da fara wasan, Thomas Muller na Jamus ya samu nasarar fara jefa kwallo a ragar Argentina. Ko da yake 'yan wasan Argentina sun yi ta kai hari, amma ba su iya zura kwallo a ragar Jamus ba. Duk da haka, bayan an dawo hutun rabin lokaci, Miroslav Klose na Jamus ya sa kwallaye 2 a ragar Argentina, wanda karo na 100 ne ya wakilci Jamus domin shiga gasannin duniya. Haka kuma, Arne Friedrich na Jamus shi ma ya sanya kwallo a ragar Argentina.
Bayan karawar, Klose ya buga kwallaye 14 a gasar cin kofin duniya, wato ke nan yawan kwallayen ya yi daidai da yawan kwallayen da wani mai kai hari na daban na Jamus Gerhard Muller ya buga a gasar, sa'an nan, ya zama na biyu a tarihin gasar bayan Ronaldo na kasar Brazil, wanda ya buga kwallaye 15 gaba daya.
Har wa yau, a wata karawa ta daban da aka yi a tsakanin Spaniya da Paraguay, David Villa na Spaniya shi ne ya zura kwallo a ragar Paraguay, wadda hakan ya taimaka wa Spaniya a karo na farko ta shiga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya. Haka zalika, bisa kwallaye 5 da ya jefa, David Villa ya zama na farko a gasar cin kofin duniya ta Afirka ta Kudu. (Tasallah)