A cikin nasa jawabi, Mr. Bernard Makuza ya ce, "Yau ina farin cikin halartar wannan bikin murnar ranar rumfar kasar Rwanda da aka shirya a yayin EXPO na Shanghai. Da farko dai, na wakilci shugaban kasarmu Paul Kagame da dukkan jama'ar kasar Rwanda, na nuna gaisuwa cikin sahihanci ga shugaba da jama'ar kasar Sin."
Sannan Mr. Makuza ya ce, ko da yake ban dade ina nan kasar Sin ba, amma na riga na san nasarar da kasar Sin, musamman jama'ar birnin Shanghai, suka samu wajen shirya bikin EXPO na shekara ta 2010. Mr. Makuza ya kuma nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da ta taimaki kasar Rwanda da sauran kasashen Afirka wajen halartar bikin EXPO na Shanghai.
Bayan bikin murna, mawaka da 'yan kada ganga na kasar Rwanda sun rera wa mahalarta wasu wakoki da kuma taka raye-raye. Yau da dare, za su kuma nuna wasu wasannin kwaikwayo ga masu yawon bude ido na kasar Sin. (Sanusi Chen)