in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uruguay ta samu nasara a kan Ghana yayin da Holand ta doke Brazil
2010-07-03 21:40:34 cri
A jiya 2 ga wata, a gasar cin kofin duniya da ke gudana a kasar Afirka ta Kudu, Kasar Uruguay ta lallasa Ghana da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Nasarar da Uruguay ta samu ya ba ta damar tsallakewa zuwa zagayen kusa da na karshe.Tun da farko dai sai da aka yi karin lokaci a wasan bayan an tashi kunnen doki 1 da 1 a mintuna casa'in na farko.Dan wasan Ghana Asamoah Gyan ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga a mintin karshe na wasan.

Kafin haka kuma, a filin wasa na Nelson Mandela, Holand ta doke Brazil da ci biyu da daya, hakan ya ba kasar Holand damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba, inda za ta hadu da kasar Uruguay.

Brazil ce ta fara zira kwallo a minti goma da fara wasan, sai bayan an dawo daga hutu sannan Holand ta rama.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da ake lashe Brazil a zagayen dab da na kusa da karshe, bayan da ta fita a irin wannan mataki a gasar da ta gabata. Holand dai ba ta taba lashe gasar cin kofin duniya ba a tarihin kwallon kasar, kuma tana fatan kafa sabon tarihi a Afrika ta Kudu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China