in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ranar rumfar kasar Burundi a bikin EXPO na Shanghai
2010-07-03 17:30:33 cri
Ranar 3 ga wata, rana ce ta rumfar kasar Burundi a birkin baje-kolin kasa da kasa dake gudana a birnin Shanghai. Ministan harkokin wajen kasar Burundi Augustin Nsanze, tare da babban wakilin gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin bikin EXPO na Shanghai Hua Junduo sun halarci bikin, inda kuma suka gabatar da jawabi.

A nasa bangaren, Mista Augustin Nsanze ya ce, rumfar kasar Burundi dake dakin-nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka tana kokarin nunawa masu kallo dimbin albarkatu da Allah ya horewa kasar, da irin kyan-ganin da take da shi. Kamar yadda babban taken rumfar Burundi yake, wato "kasancewar dan Adam da muhalli tare", gwamnatin kasar tana aiwatar da manufar raya masana'antu da birane tare da kiyaye muhallin halittu. Mista Augustin ya ce:

"A rumfar kasar Burundi, masu kallo suna iya ganin cewa, ana samun yanayi mai kyau, da ni'imtattun wurare, gami da dabbobi da tsire-tsire iri-iri a Burundi. Muna fatan mutanen kasashe daban-daban za su zuba jari a kasarmu, haka kuma gwamnatinmu ta amince da dokoki da dama da suka shafi zuba jari da karbar haraji, a kokarin baiwa mutane kwarin-gwiwar zuba jari a kasar Burundi."(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China