A bana, za a yi kwaskwarima ga yankunan kananan rumfuna guda 21 dake yankin titin Bahaer a birnin Urumqi na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uighur. Kafin ya kaura, Zhang Chunxian, sakataren JKS na jihar Xinjiang ya shiga gidan Maimaiti Nuer dake titin Bahaer domin yin hira da shi. Kuma Zhang ya tambaye shi cewa, ko ya amince da yawan karin kudin da ya samu a matsayin diya sabo da kaurar da suka yi, ko kuma akwai wasu kayayyaki da yake bukata a sabon gidan?
Maimaiti ya bayyana cewa, "Babu saura sai dai ina fatan za a ba da karin kudi bisa fadin gidana."
Zhang ya ce, "Da kyau! Bayan an rushe wadannan kananan rumfuna, za a kafa sabbin gidaje a wurin, kuma yanayin rayuwa zai samu kyautatuwa. Watakila za mu sake kawo ziyara a gidanka kamar yadda muke a saba yi, watakila za mu sake zuwa bayan shekaru 2 masu zuwa."