in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mu zagaya rumfar kasar Somaliya a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-06-30 17:30:55 cri
Batun'yan fashin teku ya jawo hankalin duniya a kan kasar Somaliya wadda ke gabashin nahiyar Afirka. Yanzu haka idan an ambaci Somaliya, watakila 'yan fashin teku da ke mashigin tekun Aden ne za a tuna da su. Amma hasali ma dai, wannan ba cikakkiyar masaniya ba ce a kan kasar. Ranar 26 rana ce ta rumfar kasar Somaliya a farfajiyar bikin bajen kolin kasa da kasa da ake yi a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Abubuwan da aka nuna sun kara fadakar da jama'a a kan kasar ta Somaliya daga fannoni daban daban.

Da ka shiga rumfar Somaliya, za a ga mutum mutumin rakuma hudu da suka fi daukar hankalin jama'a. Kasancewarta kasar da ke dogara ga aikin kiwon dabbobi ta fannin tattalin arziki, yawan rakuman da ake kiwo a Somaliya ya kai kashi 30% na duk duniya.

Zhang Dan, wadda ta zo daga lardin Anhui na kasar Sin, ta dauki hoto tare da mutum mutumin rakuma cikin murna da farin ciki, kuma ta ce, "ban yi tsammanin ganin rakuma a Somaliya ba. Ma'aikatan rumfar sun ce mini, a kasar Somaliya, a kan gai da juna tare da al'adar tambayar cewa, 'ko rakuma suna lafiya?'"

Ma'aikatan rumfar sun bayyana mana cewa, tun da aka bude bikin baje kolin, rumfar Somaliya na daya daga cikin rumfunan hadin kan Afirka da suka fi jawo masu ziyara. Amma ba wai rakuma ne kawai ke jawo su, a'a, har da kasar da ke ba jama'a mamaki.

A jikin bangon rumfar, an sanya manyan hotuna da ke nuna zaman rayuwar mutanen Somaliya da al'adunsu da yanayin kasar da kuma halittunta. Sa'an nan, bisa kide-kide masu ban sha'awa na Somaliya da ake nunawa a wani video na bayyana tarihi da al'adu na Somaliya. Somaliya na da dadadden tarihi da ingantattun al'adu, tuni yau da shekaru fiye da 1700 da suka wuce, aka kafa kasar Puntland a wurin.

Xia Hua, wani malamin da ya zo daga lardin Jiangsu da ke kudancin kasar Sin, wanda ya zagaya rumfar tare da iyalansa, ya ce mana, "bayan da na zagaya rumfar, na kara fahimtar al'adun gargajiya na Somaliya, kuma 'yan fashin teku abu ne na wasu tsirarrun mutanen kasar kawai."

Duk da nisan da ke tsakanin Somaliya da kasar Sin, akwai alaka ta musamman tsakanin kasashen biyu. Tuni a karni na 14, shahararren matukin jirgin ruwa na daular Ming ta gargajiyar kasar Sin, Zhenghe ya taba kai ziyara Somaliya tare da ayarinsa da kuma kayayyakin fadi-ka-mutu da siliki iri iri na kasar Sin. Har ma a kasar Somaliya, akwai wani kauyen da ake kira Zheng He, kuma an ce, mutanen wannan kauye zuriyoyi ne da suka fito daga mutanen wannan ayarin jiragen ruwa.

A shekarun 1960 kuma, tsohon firaministan kasar Sin, marigayi Zhou Enlai ya kai ziyara Somaliya, ziyarar da ta karfafa dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Har wa yau kuma, Somaliya kasa ta farko ce a gabashin Afirka da ta kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, kuma yau shekaru 50 ke nan.

Halartar wannan bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi a birnin Shanghai karo na farko ne da Somaliya ta halarci wani bikin baje kolin duniya. Shugaban kwamitin kula da man fetur da makamashi na Somaliya ya bayyana a gun bikin murnar ranar rumfar cewa, bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi a Shanghai wani kasaitaccen biki ne, kuma Somaliya na iya koyon yadda za a iya raya zaman al'umma da ke da muhalli mai kyau da kuma samun dauwamammen ci gaba.

Yaki da tashin hankali sun tsunduma Somaliya cikin talauci, amma duk da haka, ba su iya hana jama'ar kasar neman zaman rayuwa mai inganci. A gun bikin EXPO na Shanghai, Somaliya ta nuna al'adunta, tare da yin musayar ra'ayoyi da sauran kasashe dangane da ci gaban birane. "Somaliya za ta yi iyakacin kokarin gaggauta ci gaban biranenta cikin daidaici duk da wahalhalun da take fuskanta." In ji shugaban kwamitin kula da mai da makamashi na Somaliya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China