A cikin jawabinta, madam Hasna ta bayyana cewa, dakin Djibouti zai gwada al'adun gargajiya da ni'imtattun wuraren kasar yadda ya kamata. Da fatan bikin baje kolin zai samu babbar nasara.
Wang Wenzhang ya bayyana cewa, ya yi imani cewa kasar Djibouti za ta zama hasken bikin baje kolin bisa alamar kanta.
A bikin ranar dakin Djibouti, masu nuna fasahohi na kasar sun yi shirye-shirye ga masu kallo.
Taken dakin Djibouti shi ne "Djibouti---cibiyar tattalin arziki", inda aka gwada albarkatun yawon shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa ta duniya.(Fatima)