in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsugunar da jama'a a lokacin da ake yin ayyukan sufurin ruwa daga kudu zuwa arewa na kasar Sin
2010-06-29 14:06:24 cri
Ibrahim: Yayin da aka soma shiga lokacin zafi a nan kasar Sin, kuma lokaci ne da manoma suke fara yin girbin alkama. Yayin da ya kalli alkama da ke cikin gonaki, manomi Huang Chaohai, mai shekaru 48 da haihuwa, ya yi farin ciki sosai ya ce. "A da, mu kan noma lemo kawai, kuma yawan kudin da muka samu ya kai kimanin kudin Sin yuan dubu 20 a kowace shekara. Bayan na koma wannan kauye, na samu gonakin da yawansu ya kai hekta 10, inda nake noman masara da alkama. Sabo da haka, yawan kudin shiga da zan iya samu zai kai kimanin kudin Sin yuan dubu 50 a kowace shekara."

Sanusi: A da, garin Huang Chaohai yana cikin wani kauye na birnin Danjiangkou na lardin Hubei ne, amma a watan Maris na bana, ya koma karkashin kauyen Lijia da ke birnin Xiangfan da manoman da yawansu ya kai 170 ko fiye. Sun bar garinsu sun koma wani sabon wuri domin wani muhimmin aiki, wato aikin sufurin ruwa daga kudu zuwa arewa da ake yi a nan kasar Sin. Garinsu zai zama wurin da za a gina wata babbar madatsar ruwa.

Ibrahim: A nan kasar Sin, yawan ruwa da ke kudu da wanda ke arewa ya sha bamban sosai, a zahiri ma ana karancin ruwa a yankunan arewacin kasar. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin yin wani aikin sufurin ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar domin magance matsalar karancin ruwa da ake fuskanta a yankunan arewacin kasar. A shekara ta 2002 ce aka soma wannan aiki. Bisa wannan shiri, za a yi sufurin ruwa daga madatsar ruwa ta Danjiangkou ta lardin Hubei zuwa biranen Beijing da Tianjin, kuma tsawon hanyar sufurin ruwa daga madatsar ruwa ta Danjiangkou zuwa Beijing da Tianjia ya kai kilomita 1267.

Sanusi: Bisa bukatar da ake da ita domin kara girman madatsar ruwa ta Danjiangkou, dole ne a tsugunar da mutanen da wannan aiki zai shafa da yawansu ya kai dubu daruruwa. A da, galibinsu sun yi zama a yankuna, inda ba a iya samun saukin zirga-zirga, balle bunkasuwar tattalin arziki. Bayan an mai da su zuwa wasu kyawawan wurare, sun kuma samu kyakkyawan sharadin samun abin kashewa. Alal misali, Huang Chaohai yana da wani gida mai benaye biyu, kuma mai dakuna 3 da ke karkarar wani gari, kuma ke kusa da wata hanyar mota.

Ibrahim: An bayyana cewa, an tsugunar da wadannan mazauna a wurare 194 da ke gudummomi da birane 21. An zabi wadannan wurare ne bisa ra'ayoyin wadannan mazauna. Mr. Wang Yuanliang wanda ke kula da aikin tsugunar da jama'a a lardin Hubei ya bayyana cewa, "Tsugunar da mazauna aiki ne da ke da nasaba da mutane. A farkon lokaci, mun zabi wurare 510 wadanda suke gundumomi da birane 29. Mazauna su na iya zuwa wuraren da suke son zuwa. Sannan ba mu iya soma gina gidajen kwana ba kafin jama'a su sa hannu a kan hotunan gidajen da aka zana."

Sanusi: Ba ma kawai mazaunan da aka tsugunar da su suna da ikon zabar wuraren da suke son zuwa ba, har ma suna da ikon sa ido kan yadda ake gina gidajensu na kwana. Mr. Zhang Yonglong, na daya daga cikin wakilai biyar na kauyen Jiangkou na birnin Danjiangkou. Dole ne kowanensu ya yi kwanaki 10 yana sa ido kan yadda ake gina gidaje har zuwa lokacin da za a gama gina gidajen. Zhang Yonglong ya ce, "Wannan gida ne mai inganci, muna farin ciki sosai. A hakika dai, a da mun gina gidaje ne da katako da wasu tubala, ba mu yi amfani da ingantaccen karfe da siminti ba. Sabo da haka, yanzu ba mu da damuwa dangane da ingancin wadannan sabbin gidajen kwana."

Ibrahim: He Huaijun wanda yake zaune a kauyen Yaowan na birnin Danjiangkou, shi da iyalinsa za su koma garin Gucheng na birnin Xiangfan. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "A garinmu, mu kan noma itatuwan lemo da kiwon kifaye. Lokacin da muke zaune a garinmu, na noma itatuwan lemo a gonakin da yawansu ya kai kusan hekta 1. Bisa manufar gwamnati, yawan kudin diya da gwamnati ta ba ni ya kai kudin Sin yuan dubu 93 da dari 6 ga kowace hekta. Sabo da haka, na samu kudin diya daga hannun gwamnati da yawansu ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu 70. Bugu da kari, gwamnatin wuri ta ba ni kudin diya ga sauran kadarorina, kamar su aikin kiwon kifaye da rijiya da itatuwan da na dasa a kewayen gidana. A hakika dai, ina farin ciki sosai." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China