in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin Hu Jintao da Lee Myung-bak
2010-06-28 09:41:01 cri

A ranar 27 ga wata a birnin Toronto, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Korea ta kudu Mr Lee Myung-bak.

Yayin ganawa, Hu Jintao ya nuna cewa, Sin tana fatan yin hadin kai tare da Korea ta kudu domin ingiza dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.

Mr Hu Jintao ya jadadda cewa, a matsayinsu na kasashen mafi girma ta fuskar tattalin arziki a gabashin Asiya har ma da duniya baki daya, kamata ya yi kasashen Sin da Korea ta kudu su yi hadin kai domin kawo moriyar juna.

A nasa bangaren, Lee Myung-bak ya ce, a watan Nuwamba na bana, Korea ta kudu za ta shirya taron koli na G20 a karo na biyar, kuma kasar tana fatan hada kai da Sin domin tabbatar da samun nasara a taron. Ban da wannan kuma, ya ce, Korea ta kudu na dora babban muhimmanci kan dangantakar hadin kai ta sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, a sabili da haka, tana fatan kara hada kai da Sin.

Game da halin da ake ciki a zirin Korea, Hu Jintao ya nuna cewa, Sin ta kan zura ido kan lamarin, kuma tana kokarin samar da zaman lafiya mai karko a zirin a matsayin abu na farko a duk lokacin da aka tabo lamarin. Kasar Sin ta yi Allah wadai da dukkan matakan da aka dauka na wargaza zaman lafiya da karko a zirin. Dadin dadawa, ya ce, saboda mawuyancin halin da ake ciki, kamata ya yi, bangarorin daban-daban da abin ya shafa su yi la'akari da halin da ake ciki, su kwantar da hankalinsu. Hu Jintao ya ce, ya kamata, a warware duk wata matsala bisa tushen yin la'akari da moriyar jama'ar zirin. Kasar Sin tana fatan kara yin mu'amala kan lamarin tare da Korea ta kudu.

Lee Myung-bak kuma ya ce, Korea ta kudu tana nuna babban yabo ga matakin da Sin ta dauka wajen tabbatar da yin watsi da makaman nukiliya a zirin. Korea ta kudu tana fatan yin musayar ra'ayoyi kan lamarin tare da kasar Sin.
A wannan rana da yamma, Mr Hu Jintao ya bar birnin Toronto domin dawowa kasar Sin bayan ya halarci taron koli na G20 a karo na hudu da yin ganawa tsakaninsa da Mr Lee Myung-bak.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China