in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya ba da shawarwari 3 wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2010-06-28 09:03:20 cri

A ran 27 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao da ya halarci taron farko na taron koli karo na 4 na shugabannin kasashe membobin kungiyar G20 ya yi wani jawabi mai taken "yin kokarin samun kyakkyawar makoma", inda ya ba da shawarwari 3 wajen sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa yadda ya kamata, da kuma kafa wani tsarin hada-hadar kudi na duniya don inganta tattalin arziki.

Shawarwarin sun hada da sa kaimi ga kungiyar G20 da ta kasance muhimmin dandalin inganta hadin gwiwar tattalin arzikin duniya a madadin tsarin tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya, da gaggauta kafa sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya mai adalci, da kuma sa kaimi ga inganta tsarin cinikin duniya cikin 'yanci.
Hu Jintao ya jaddada cewa, akwai ayyuka masu yawa da za a gudanar wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa yadda ya kamata, ba ma kawai za a ci gaba da yin ayyukan ba, hatta ma a yi la'akari da halin da kasa da kasa suke ciki, da girmama hanyoyi daban daban wajen samun bunkasuwar kasashen duniya.

Ban da wannan, Hu Jintao ya bayyana cewa, kungiyar G20 tana da alhakin kara samar da karfin siyasa da hukumomin kudi da kuma wasu tsari don warware matsaloli da suka shafi aikin samun bunkasuwa. Kamata ya yi bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da sauran hukumomin kudi na duniya su ba da taimako ga kasashe masu tasowa musamman kasashe marasa ci gaba.

A madadin gwamnatin kasar Sin, Hu Jintao ya yi alkawarin ci gaba da ba da taimako ga kasashe masu tasowa a karkashin tsarin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa don taimakawa kasashe masu tasowa su samu bunkasuwa.

Kazalika Hu Jintao ya kara da cewa, ya kamata a kafa ma'aunin bai daya na tabbatar da matsayin samun shugabanci cikin adalci, ta haka sakamakon da aka samu bisa ma'aunin zai bayyana halin tattalin arziki da wata kasa ke ciki da matsayin shugabancinta.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China