in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin Hu Jintao da Naoto Kan
2010-06-28 09:02:08 cri

A ranar 27 ga wata a birnin Toronto, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Japan Mr Naoto Kan

Yayin ganawar, Hu Jintao ya nuna cewa, kasar Sin tana dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan yin hadin kai da kasar Japan domin yin amfani da zarafi mai kyau ta yadda za su ingiza dangantakar kawo moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu a karkashin yarjejeniyoyi hudu da suka kulla ta fuskar siyasa a tsakaninsu.

Mr Hu Jintao ya ba da shawarwari 5 domin kara bunkasa dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

Ban da wannan kuma, Mr Naoto Kan ya ce, gwamnatin kasarsa ta kan bunkasa dangantaka a tsakanin kasashen biyu bisa yarjejeniyoyi budu da suka kulla a tsakaninsu ta fuskar siyasa. Kasar Japan tana fatan yin hadin kai tare da kasar Sin domin kara yin musayar ra'ayoyi ta fuskar jam'iyyu da majalisu da hukumomi daban-daban da yin mu'amala a dukkan fannoni, da kuma bunkasa dangantakar cinikayya ta kawo moriyar juna a tsakaninsu yadda ya kamata, da sa kaimi ga hadin gwiwa da aka yi a yankin gabashin Asiya da warware wasu matsalolin da suka bullo a tsakaninsu.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China