Kamar yadda aka tanada, shugabannin kasashe daban daban za su tofa albarkacin bakinsu daya bayan daya dangane da babban taken taron na 'farfadowa da sabon mafari', inda shugaba Hu Jintao zai zama na biyu wajen gabatar da jawabi. Kafin haka kuma, Hu ya yi nuni da cewa, game da taron da ake yi kasar Sin na da bukatu 4, wadanda suka hada da kara yin mu'amala kan manyan tsare-tsaren tattalin arziki don tabbatar da farfadowar tattalin arzikin duniya, da yin kokarin gyara tsarin hukumar IMF don kara yin wakilci ga kasashe masu tasowa, da kara mai da hanakli kan batun ci gaba, gami da yin kokarin kau da matakan kariyar ciniki iri daban daban. (Bello Wang)