A nasa bangaren kuma, shugaba Obama ya furta cewa, yana farin cikin ganin ci gaba da aka samu wajen raya hulda a tsakanin Amurka da Sin a 'yan shekarun baya. Hadin kan bangarorin biyu na da makoma mai kyau, ya kamata su inganta hadin gwiwarsu domin samun ci gaba baki daya.
A ran nan kuma, shugaba Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan taron koli a karo na hudu na rukuni na G20 zai samu kyawawan sakamako a fannoni daban daban. Ya jaddada cewa, yanzu tattalin arzikin duniya yana samun farfadowa, amma tushensa ba shi da inganci sosai. Kasar Sin tana son kara inganta samun daidaitawa a tsakaninta da kasar Rasha a karkashin tsarin G20 domin bayar da gudummawa ga samun dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.
A wata sabuwa kuma, a wannan rana, shugaba Hu Jintao ya gana da firaminista David Cameron na kasar Birtaniya, inda shugaba Hu ya jaddada cewa, Sin da Birtaniya suna da moriya daya wajen sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya da tinkarar kalubalen da ke gaban duniya a sakamakon kasancewar illar da matsalar kudi ta duniya da matsaloli daban daban na duniya ke bayarwa. Muddin bangarorin biyu suka kara tattaunawa a tsakaninsu, da lura da abubuwan da suke mai da hankali a kai, kana da warware rikicin da ke tsakaninsu yadda ya kamata bisa tushen nuna girmamawa ga juna da yin zama daidai wa daida, to tabbas ne za a ciyar da huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Birtaniya bisa manyan tsare-tsare gaba.(Kande Gao)