Mr. Lan ya fadi haka ne a yayin da yake halartar bikin bude taron dandalin tattaunawar karo na 2 kan sabbin nau'o'in kafofin yada labaru da yayata al'adun kabilu. Lan ya kuma kara da cewa, sabbin nau'o'in kafofin yada labaru, kamar yanar gizo na iya yayata al'adun kananan kabilu cikin sauri da sauki kuma ba tare da samun matsalar lokaci ba. Nan gaba wajibi ne kasar Sin ta sa kaimi kan yin amfani da sabbin nau'o'in kafofin yada labaru cikin harsunan kananan kabilu, da zummar yayata al'adunsu yadda ya kamata, ta yadda za su iya cin gajiyar bunkasuwar fasahar sabbin nau'o'in kafofin yada labaru. (Tasallah)