A cikin jawabinsa, Jiang Zhengyun ya waiwayi baya kan dankon zumunci irin na gargajiya dake tsakanin kasashen Sin da Somaliya. Ya yi imani da cewa, dakin nune-nune na Somaliya zai zama wata babbar alama ga bikin baje kolin.
Bayan haka, a cikin jawabinsa, Abdullahi Yussuf Ahmed ya nuna godiya ga kasar Sin da ta kula da tawagar Somaliya yadda ya kamata. Ya ce, a bikin baje kolin, kasar Somaliya za ta nuna al'adunta a duk fannoni, tare da yin musayar fasahohin bunkasa birane da sauran kasashe. Ya yi imani cewa, bikin baje kolin duniya da ake yi a birnin Shanghai a shekarar 2010 zai samar da wata kyakkyawar makoma ga Bil'adam baki daya.(Fatima)