in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da kungiyoyi 16 da suka shiga zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya
2010-06-26 16:37:09 cri

Ran 25 ga wata bisa agogon kasar Afirka ta Kudu, an kammala duka karawaer rukuni-rukunin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da ke gudana a kasar.

A cikin rukuni na G, ko da yake kungiyoyin kasashen Brazil da Portugal sun tashi 0 da 0 a karawa ta karshe, amma duk da haka sun tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar.

Sa'an nan ko da yake kungiyar Ivory Cost ta doke kungiyar kasar Koriya ta Arewa da ci uku da nema, amma an fitar da ita daga gasar. Ita dai Ivory Cost tana so Brazil ta doke Portugal ne ta samu damar tsallakewa, amma hakika ko da an doke Portugal, to, ba za ta tsallake ba, domin kwallaye tara take bukata.

Wannan sakamako na rukunin G ya nuna cewa, yanzu kungiyar kasar Ghana ce kawai ta tsallake zuwa zagaye na biyu daga cikin kasashe shidan da suka fito daga nahiyar Afrika.

A rukuni na H kuma, kungiyoyin kasashen Spaniya da Chile sun tsallake zuwa zagaye na biyu.

Ta haka an tabbatar da kungiyoyi 16 da za su kara da juna a zagaye na biyu a cikin gasar. Yau 26 ga wata, agogon Afirka ta Kudu, Ghana za ta kara da Amurka, yayin da Uruguay da Koriya ta Kudu za su kara da juna. Sa'an nan Argentina da Mexico za su kara da juna. Jamus za ta kara da Birtaniya, Holand za ta kara da Slovakia, Paraguay za ta kara da Japan, Brazil za ta kara da Chile, kuma Spaniya za ta kara da Portugal. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China