in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyautar da Maradona ya samu a ranar iyaye maza
2010-06-26 16:43:44 cri

"Wannan ne kyautar da 'yata ta ba ni a ranar iyaye maza." In ji Diego Armando Maradona.

A kowane lokaci, Maradona bai taba yin latti a gun taron manema labaru da aka shirya bayan bude gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya ba. Haka lamarin ya kasance a ran 21 ga wata a Pretoria. Bugu da kari, da fara taron manema labarun, sai Maradona ya nuna kyautar da ya samu daga 'yarsa domin murnar ranar iyaye maza, wato tabarau irin na kare hasken rana. A kasar Afirka ta kudu, akwai hasken rana sosai. A sabili da haka, wasu na amfani da tabarau. Maradona ya yi alfahari sosai har ya nuna wannan kyauta. Har ma ya sa wannan tabarau domin 'yan jarida suka dauki hotuna. Bayan taron manema labarun kuma, ya yi hira da manema labaru na gidan telibijin tare da saka wannan tabarau.

Game da Maradona, cike yake da labarai iri-iri. Amma hakan bai biya bukatunsa ba. Ya kan jawo hankalin jama'a ta hanyar bayyana wasu abubuwa masu ban al'ajabi. Duk da haka, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce ne, ya fara jawo hankalin jama'a ta hanyar amfani da wasu kayayyaki. Misalai, bayan taron manema labaru bayan karawa tsakanin kungiyar Argentina da ta Koriya ta Kudu, Maradona ya fid da wata wasika daga aljihunsa a kokarin neman afuwa daga wajen Michel Platini. Yayin da yake jagoranci a yayin wasan kwallon kafa, ya kan sa warwaron hannu. A sa'i daya kuma ya kan sa agogon hannu guda daya a kowane daga cikin hannayensa. Duk da haka, Maradona ya bayyana soyayya ga diyarsa da jikoki mata ba tare da boye komai ba. A yayin gasar cin kofin duniya, Maradona ya je Pretoria tare da diya da jikokinsa. Bayan kowane wasa da horo, ya kan zaune tare da su.

Bayan diya da jikoki, Maradona yana kula da Messi kamar yadda zai yi ga dansa. Ko da yake kawo yanzu dai Messi bai saka kwallo ba a gasar cin kofin duniya, amma Maradona ya bayyana wa 'yan jarida cewa, ya taki sa'a sosai sabo da kungiyar tana da Messi. Ya ce,

"A ganina, kamata ya yi mu kara samarwa da Messi lokacin hutu. Idan kana da wani dan wasa mai kwarewa sosai kamar Messi, kuma idan ba ka nuna masa amincewa wajen shiga kungiyar wasan kwallon kafa ko kuma shiga gasar cin kofin duniya ba, to kamar kana aikata laifi ne! Bai kamata mu kaskauta shi a yayin gasar ba, wanda hakan zai iya canza sakamakon gasar."

Sau da dama Maradona ya bayyana cewa, kungiyar Argentina ce za ta yi nasara a gasar cin kofin duniya a wannan karo da ake yi a kasar Afirka ta kudu, a sakamakon kasancewar Messi. A zuciyar wannan tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa, babu kowa sai Messi wanda yake cewa zai kai matsayinsa yadda ya kamata. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, Brazil ta lashe Cote d'Ivoire, yayin da Italiya ta yi kunnen doki da New Zealand da ci daya da daya. Bayan haka, kungiyar Faransa ta dakatar da horar da 'yan wasa. Game da wadannan batutuwa, Maradona ya bayyana ra'ayinsa da cewa,

"Kungiyar Brazil za ta shiga mataki mai zuwa ba makawa, har ma za su yi amfani da hannaye. Kungiyar Faransa ba ta kasance cikin yanayi mai kyau ba. Kungiyar Spaniya tana wasa yadda ya kamata, yayin da kungiyar Jamus ta kan nuna fifiko. Game da kungiyar Italiya, babu wanda ya san me ya faru!"

Wani dan jarida na kasar Brazil ya tashi ya tambayi Maradona cewa, mene ne ra'ayinsa game da kwallon da dan wasan kungiyar Brazil Luis Fabiano ya ci da aka nuna tababa cewa, kila ya yi amfani da hannu a gasar tsakanin kungiyar Brazil da ta Cote d'Ivoire? Mutane sun yi dariya. Amma Maradona, wanda ya taba cin kwallo a gasar cin kofin duniya a shekarar 1986 ta amfani da hannunsa ya amsa wannan tambaya ba tare da la'akari da ita ba cewa,

"Fabiano wani dan wasa ne mai cike da karfin kai hari. A gasar, kowa ya gano cewa, Fabiano ya buga kwallo da hannunsa. A bayyane, ya taba kwallo da hannu har sau biyu."

Ma'anarsa ta fito fili, wato babu wanda zai yi daidai kamar yadda Maradona ya yi a shekarar 1986.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China