in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Toronto domin halartar taron kolin G20
2010-06-26 16:24:03 cri

A ranar 25 ga wata da yamma, agogon Canada, shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya isa birnin Toronto, inda zai halarci taron kolin kungiyar G20 da za a gudanar daga ranar 26 zuwa 27 ga wata. Taron kolin da za a kira zai kasance na farko tun bayan da aka mayar da taron a matsayin wani tsari na kungiyar, sabo da haka, yana da muhimmiyar ma'ana.

Shugaban kasar Sin zai halarci taron tare da sauran shugabannin mambobin kungiyar ta G20, ciki har da shugaban kasar Amurka, Barack Obama, shugaban kasar Rasha, Dmitry Medvedev, sabon firaministan kasar Japan, Naoto Kan. Har wa yau kuma, jami'an kungiyoyin duniya da suka hada da asusun ba da lamuni na duniya da bankin duniya, tare kuma da shugabannin wasu sauran kasashe su ma za su hallaci taron. Halin da tattalin arzikin duniya ke ciki da matsalar basusuka da kasashen Turai ke fuskanta za su zama muhimmin batun da za a tattauna a yayin taron.


A lokacin taron, shugaban kasar Sin, Hu Jintao zai gabatar da muhimmin jawabi, kuma bisa ga labarin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar, an ce, kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su iya daidaita manufofin tatatlin arziki da sa kaimi ga gyare-gyaren asusun ba da lamuni na duniya ta fuskar kason kasa da kasa da kuma gyare-gyaren aikin sa ido kan harkokin kudi, haka kuma tana kin yarda da kariyar ciniki.

Kafin zuwansa Toronto, Hu Jintao ya kuma gana da shugaban majalisar dattawa ta Canada, Noel A.Kinsella, da shugaban majalisar wakilai ta kasar, Peter Milliken, a birnin Ottawa, wadanda kuma suka bayyana burinsu na tattauna batun ingancin abinci a kasar Sin.(Lubabatu)
 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China