in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moriyar bai daya da ke tsakanin Sin da Kanada ta fi sabanin ra'ayi, in ji Hu Jintao
2010-06-25 17:49:47 cri
A ranar 24 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya halarci liyafar da Stephen Harper, firaministan kasar Kanada, ya shirya masa a birnin Ottawa na kasar, inda Hu ya yi wani muhimmin jawabi mai taken 'Yin kokarin kyautata huldar abokai ta manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasar Sin da kasar Kanada daga dukkan fannoni'. Cikin jawabin, Hu ya jaddada cewa, ko da yake yanayin da kasashen 2 ke ciki ba iri daya ba ne, amma duk da haka babu rarrabuwar kai a tsakaninsu dangane da ainihin moriyarsu, sa'an nan moriyar bai daya da ke tsakaninsu ta fi sabanin ra'ayi.

A ran nan, jami'an gwamnatocin 2 da masu sana'ar cinikayya da masana'antu fiye da 500 sun halarci liyafar, inda suka ji yadda shugaba Hu Jiantao na kasar Sin ya nuna yabo ga kokarin kyautata huldar bangarorin 2 da ake yi a kai a kai bayan da kasashen 2 suka kulla huldar diplomasiyya shekaru 40 da suka wuce. Hu ya kara da cewa, 'A hakika dai, ci gaban huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Kanada ba kawai tana amfana wa jama'ar kasashen 2 ba, har ma ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, hade da walwala a shiyyar Asiya da tekun Pasific, har ma duk duniya.'

Shi ya sa, shugaba Hu ke ganin cewa, kamata ya yi, kasashen 2 su tantance manyan tsare-tarensu tare da nuna hagen nesa, sa'an nan su tsaya kan matsayinsu na tabbatar da huldar kawaye, gami da yin kokarin kyautata huldar da ke tsakaninsu.

Ta la'akari da yanayin da kasashen 2 ke ciki ta fuskar yin cinikayya tsakaninsu, wanda bai samu ci gaba sosai ba tukuna, abin da ya sa shugaba Hu ke ganin cewa, akwai ayyuka da dama da bangarorin 2 za su iya yi domin inganta hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Sa'an nan, don neman kara girman tsarin hadin gwiwar, daga matsayinta, hade da habaka ta zuwa fannoni daban daban, Hu ya samar da shawarwari 5, wadanda suka hada da habaka cinikayya, da inganta zuba jari ga juna, da zurfafa hadin kai da ake yi ta fuskar makamashi da albarkatun kasa, da habaka hadin gwiwa zuwa wasu sabbin fannoni, da kuma kokarin kau da kariyar ciniki. Shugaba Hu ya kara da cewa, 'Kasar Sin ta nuna farin ciki ga matakan da gwamnatin kasar Kanada ta dauka na kara yin ciniki tare da kasashe daban daban, da kuma habaka cinikayyar da take yi da kasar Sin. Kasar Sin ba za ta yi kwadayin neman samun rarar kudi a wajen cinikayyar da take yi da Kanada ba, sa'an nan tana so ta kara shigo da wasu kayayyakin kirar Kanada, wadanda kasar ke kan gaba wajen sarrafa su, musamman ma kayayyaki masu fasahohin ci gaba. A ziyarar da nake yi, ni da shugabannin kasar Kanada mun cimma ra'ayi daya kan daukar niyyar kara yawan kudin cinikkayar tsakanin kasashen 2 zuwa dalar biliyan 60 a shekarar 2015. Muna da imanin cewa, burin da aka sanya zai sa kaimi ga kokarin da muke yi na kyautata huldarmu ta fuskar tattlin arziki da cinikayya.'

Ban da wannan kuma, dangane da hadin kan kasashen 2 a fannin makamashi, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin kulla huldar kawaye ta dogon lokaci kuma mai dorewa, kamar yadda ya fadi cewa, 'Kasar Kanada tana da makamashi, da ma'adinai, da dimbin albarkatun kasa, sa'an nan kasar Sin ta kasance wata babbar kasuwa mai kyau da kullum take bukatar wadannan abubuwa, shi ya sa za a iya hangen wata makoma mai kyau wajen habaka hadin kai a wannan fanni.'(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China