in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna kide-kide da raye-raye na gargajiya daga kasar Ireland a bikin EXPO
2010-06-25 10:55:15 cri

A ran 13 ga wata, masu yawon shakatawa da suka fito daga kasashe daban daban sun ji dadin gajerun kide-kide da raye-raye masu ban sha'awa a rumfar kasar Ireland. A yayin da ake nuna wadannan kide-kide da raye-raye, 'yan kallo kimanin 200 sun zauna a kasa a gaban dandalin nuna wasanni dake wajen rumfar kasar Ireland, sun nishadantu irin kide-kide masu siffar musamman na kasar Ireland.

Shahararriyar kungiyar wasan fasaha ta Bru Boru ta kasar Ireland ita ce ta yi wannan kida mai dadin ji. An mayar da kungiyar wasan fasaha ta Bru Boru a matsayin jakadar al'adu da wasan fasaha ta kasar Ireland, ta taba nuna wasanni cikin bukukuwan EXPO da aka yi a kasashen Japan da Spaniya, kana ta taba nuna wasanni a kasar Sin sau da yawa. A kan dandali, 'yan wasan fasaha na kungiyar sun yi raye-rayen Tap na kasar Ireland a gaban 'yan kallo.

Madam Yin Jing da ta fito daga birnin Jinan na lardin Shandong ta ce, ta yi farin ciki sosai da ganin raye-rayen Tap na kasar Ireland a bikin EXPO. Ta ce,

"A lokacin da, na taba kalla irin wadannan raye-raye ta talibijin ko internet. Rawar da na kalli a karo na farko ita ce 'kaunar babban kogi", ina son wannan rawa sosai. Amma yanzu, na kara kaunar irin wannan rawa domin ganin raye-rayen Tap a bikin EXPO, wadanda suka fi burge ni."

Ban da haka kuma, raye-rayen sun jawo hankalin Mr. Hu Tiankun da ya fito daga birnin Zhengzhou na lardin Henan sosai. Ya ce,

"Kasar Ireland ta kawo mana raye-raye masu ban sha'awa dake da banbanci sosai da na kasar Sin, kana suna da dadin ji sosai. Mun yi farin ciki domin ganin irin wannan rawa a yayin da muke yawon shakatawa a farfajiyar bikin EXPO."

A hakika dai, ba ma kawai kide-kide sun burge 'yan kallo ba, hatta ma sun burge 'yan wasan fasaha da suke yin wadannan kide-kide. Wani kwararre a fannin wasan violin Finbarr Condon-English ya kasance cikin farin ciki yana cewa,

"A yayin da nike yin kide-kide a kan dandali, ina tsammani cewa, ina yada kyawawan al'adun kasarmu ga jama'ar kasar Sin. Shi ya sa, na yi namijin kokarin yin kide-kide, kuma ni ma ina jin dadinsu."

Wannan kungiyar wasan fasaha ta yi kwanaki 3 tana nuna wasanni a gun bikin EXPO na Shanghai, kana ta ci gaba da nuna wasanni a ranar rumfar kasar Ireland a cibiyar farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Bisa shirin da aka yi, an ce, yawan wasanni masu ban sha'awa da za a nuna a gun bikin EXPO na Shanghai zai kai 800, kuma za a nuna wadannan wasanni fiye da sau dubu 20. Shahararrun 'yan wasan fasaha na nahiyoyi biyar na duniya ne suke nuna wasanni masu siffar musamman da ba za a iya ganinsu ba a kasar Sin, ta haka, bikin EXPO na Shanghai ya kasance tamkar babban dandalin musayar ra'ayi kan al'adun kasashe daban daban na duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China