Yayin da Hu Jintao yake ziyara a kasar Canada, bangarorin biyu sun jaddada batun inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu, kana sun sanar da cewa, za a daga yawan kudin da ake samu daga ciniki a tsakanin kasashen biyu zuwa dala biliyan 60 a shekarar 2015, da kuma kafa cibiyar al'adun kasar Sin a kasar Canada.
Ban da wannan, yarjeniyoyin da gwamnatocin kasashen biyu suka daddale sun hada da kafa rukunin kiyaye muhalli a karkashin kwamitin hadin gwiwa na kasashen biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya, da kuma mai da tawagar yawon shakatawa ta kasar Sin ta kara samun sauki wajen yin yawon shakatawa a kasar Canada da dai sauransu.(Zainab)