in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya gana da shugabannin kasar Canada
2010-06-25 08:33:18 cri

A ran 24 ga wata da safe, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da babbar gwamnar kasar Canada Michaelle Jean a birnin Ottawa.

Hu Jintao ya ce, bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Canada ta haifar da samun moriya tsakanin jama'ar kasashen biyu, kana ta ba da taimako wajen kiyaye zaman lafiya da na karko da wadata a yankin Asiya da tekun Pasific har ma da dukkan duniya. Kasar Sin ta dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Canada, kuma tana son yin kokari tare da ita wajen kiyaye yin mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kara fahimtar juna a fannin siyasa, da yin amfani da fifiko, da kara yin mu'amala a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kimiyya da fasaha da ilmi da al'adu da kiwon lafiya da dai sauransu, da kara yin hadin gwiwa kan manyan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da yankuna, ta haka za a inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

Madam Jean ta bayyana farin cikinta domin za ta halarci bikin ranar da aka gabatar da nune-nune a rumfar kasar Canada a gun bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai na kasar Sin. Kasarta ta nuna yabo ga kasar Sin sakamakon samun nasara wajen tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya da kiyaye bunkasuwar tattalin arziki.

A ran 24 ga wata da yamma a birnin Ottawa, Hu Jintao ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Canada Stephen Harper, inda Hu Jintao ya gabatar da cewa, za a yi kokarin daga yawan kudin da ake samu daga ciniki a tsakanin kasashen biyu zuwa dala biliyan 60 a shekarar 2015.

Bayan shawarwarin, Hu Jintao da Mr Harper sun halarci bikin sa hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwarsu, ciki har da yarjejeniya game da wuraren yawon shakatawa na kasashen biyu.

A ran 24 ga wata da yamma a birnin Ottawa, Hu Jintao ya gana da shugaban jam'iyyar Liberal ta kasar Canada Michael Ignatieff da kuma tsohon firaministan kasar Jean Chretien.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China