in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin fasahohin zamani da ake nunawa a yayin bikin EXPO suna bayyana kyakkyawar makomar zaman rayuwa a birane
2010-06-24 17:40:36 cri
Fadar crystal ta kasar Ingila da hasumiyar Eiffel ta kasar Faransa da kwan fitila da akwatin talibijin da mota dukkansu sabbin fasahohi ne da aka kirkiro kuma aka nuna a gun bukukuwan EXPO daban daban da aka shirya a baya, kuma har yanzu suna yin tasiri ga zaman rayuwar bil Adam.

Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin yana ganin cewa, bikin EXPO ya zama dandalin mayar da irin wadannan fasahohin zamani su zama kayayyakin da ake iya saya ko sayarwa a kasuwa, kuma suna nuna yadda za a raya birane a nan gaba. Mr. Wan ya ce, "Da farko dai, makamashi marasa gurbata muhalli za su zama muhimman makamashin da za a yi amfani da su a birane. Sannan, za a kara mai da hankali wajen raya tattalin arzikin bola jari a birane. Bugu da kari, za a kara yin amfani da injuna masu aiki da kansu wadanda suke iya dacewa da yanayin duniya a birane. Haka kuma, sana'o'in da suke da nasaba da ilmomi za su zama muhimman sana'o'i da za a bunkasa a nan gaba a birane. Daga karshe dai, yankunan da suke da manya da kananan birene da yawa za su kara samun ci gaba."

Wasu mutane suna shakkar cewa, ko sabbin fasahohin zamani za su kawo illa ga kokarin samar da guraban aikin yi a nan gaba? Mr. Hiroshi Tsukamoto, babban wakilin rumfar kasar Japan da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai ya ce, injunan Robot da 'yan kwadago za su iya zaman kafada da kafada cikin lumana a zaman al'ummarmu.

"'Yan kwadago ba su iya jure wasu wahalhalu da suka shafi mummunan yanayin aiki. Wasu munanan yanayin aiki ba. A irin wannan lokaci, za mu iya yin amfani da injunan Robot don su maye gurbin 'yan kwadago. Har yanzu, 'yan kwadago ne suke taka muhimmiyar rawa, kuma yana da muhimmanci sosai wajen yin amfani da injunan Robot a tare. Sabo da haka, muke jaddada cewa, ya kamata a kafa hulda a tsakanin fasahohin zamani da 'yan kwadago."

Lokacin da muke jin dadin zaman rayuwar da sabbin fasahohin zamani suke kawo mana a kowace rana, mun kuma gane cewa, yawan makamashin halittun da ake amfana yanzu za su iya karewa, ba za mu iya yin amfani da su har abada ba. Madam Zhong Yanqun, mataimakiyar diraktan kwamitin zartaswa na bikin EXPO na Shanghai ta ce, sabbin fasahohin zamani da ake kirkirowa za su kara kawowa dan Adam fatan alheri, kuma za su sake sada jituwa a tsakanin dan Adam da yanayin duniyarmu. Sannan, ana bukatar dan Adam da ya ba da jagoranci kan yadda za a yi amfani da sabbin fasahohi kamar yadda ya kamata. Madam Zhong ta ce, "Lokacin da ake raya tattalin arziki bisa ka'idojin kasuwanci, yaya za a yi amfani da sabbin fasahohi a birane domin su taka rawarsu wajen ci gaban zaman al'ummarmu, kuma yaya sabbin fasahohin zamani za su iya bayar da gudummawa wajen ciyar da dan Adam gaba daga dukkan fannoni cikin 'yanci? Dukkansu matsaloli ne da ke kasancewa a gaban hukumomin gwamnatocin kasa da kasa da masana'antu da kamfanoni da kuma al'ummarmu baki daya."

Haka kuma, Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya bayyana cewa, bikin EXPO na Shanghai wani dandali ne, inda dukkan kasa da kasa suke musayar tunani da hanyoyinsu kan yadda za a tsara shirin raya da gina birane a nan gaba. Mr. Wan yana da imani cewa, irin wannan musanye-musanye na iya yin amfani wajen raya birane cikin sauri kana cikin lumana ba tare da cikas ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China